Sojojin Sudan sun ƙwato fadar shugaban ƙasa bayan shekara biyu ana fafatawa

Sudan

Asalin hoton, Sudan TV

Bayanan hoto, Kafar yaɗa labaran Sudan na ta nuna hotunan sojoji suna murna
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Sojojin Sudan sun ce sun ƙwato fadar shugaban ƙasa da ke Khartoum daga hannun dakarun RSF.

Hotuna da bidiyo da aka wallafa a shafukan sada zumunta, waɗanda kuma BBC ta tabbatar da sahihancinsu, sun nuna sojoji da ke murna suna ɗaga bindigoginsu sama, suna farinciki suna kuma durƙusawa domin yin addua.

Sojojin sun bayyana da ƙarfinsu da ƙwarin gwiwa domin ƙwato ikon babban birnin ƙasar shekara biyu bayan dakarun RSF sun fattatakesu daga ciki.

Zuwa yanzu dakarun RSF basu ce komai ba.

Kakakin sojin Sudan, Nabil Abdallah, ya bayyana a kafar yaɗa labaran ƙasar cewa sojoji sun ƙwace ikon fadar shugaban ƙasar da wasu gine-ginen ma'aikatu da ke tsakiyar birnin Khartoum.

'' Dakarunmu sun lalata bakiɗaya mayaƙan ƴan adawar da kayyaykin yaƙin su, kuma sun ƙwace wasu kayyayakin yaƙin da kuma makamai masu yawa,'' in ji Abdallah.

'' Muna tabbatar muku cewa za mu ci gaba da yaƙi har sai munyi nasara cikkakiya.''

A birnin Khartoum ne aka soma mummunar yaƙin basasar ƙasar kusan shekaru biyu da suka gabata, kuma a birnin ne aka gwabza manyan yaƙi.

Dakarun RSF ne ke riƙe da babban birnin da kuma yammacin Sudan tun da aka soma yaƙin.

Sudan

Asalin hoton, Sudan TV

Bayanan hoto, Kakakin sojin Sudan Nabil Abdallah ya ce za a ci gaba da gwabza yaƙi
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Sake ƙwato Khartoum zai kasance wata babbar nasara ga sojojin Sudan kuma zai kasance wani lokaci mai muhimmanci a yaƙin.

Sojojin Sudan ɗin sun kuma sami nasarori a wasu ɓangarori na tsakiyar Sudan a makonnin da suka gabata.

A ranar Alhamis, shaidu sun bayar da rahoton cewa an sami fashewar wasu abubuwa da aka harbo daga jirage maras matuƙa da hare-hare ta sama kusa da fadar gwamnati.

A wani bidiyo da aka wallafa a ranar asabar, kwamandan dakarun RSF Mohammed Hamdan Dagalo, wanda aka fi sani da Hamedti, ya sha alwashin kare fadar shugaban ƙasar da yankunan da ke kusa waɗanda ke ƙarƙashin ikon ƙungiyarsa.

Ya kuma yi barazanar kai wasu hare-hare a wasu birane da ke arewaci.

Ƙoƙarin samar da zaman lafiya da akayi sau da dama sun rujuge, a yayin da RSF ke alwashin ci gaba da faɗa domin ƙwato ikon muhimman wurare.

Yaƙin ya yi sanadiyyar ayyukan jinƙai mafi girma a duniya a cewar Majalisar Dinkin Duniya, inda ake zargin sojojin da kuma RSF da laifukan take haƙƙin biladama.