Morocco ta cire colombia daga gasar cin Kofin Duniya ta mata

Asalin hoton, Getty Images
Morocco ta doke Columbia da ci daya mai ban haushi, abin da kuma ya ba ta damar tsallakwa zuwa zagayen dab da kusa da na ƙarshe a gasar cin Kofin Duniya ta mata da ke gudana a Australiya da New Zealand.
Sakamakon na nufin cewa Jamus ta kasa fitowa daga rukunin inda ta yi kunnen doki da Koriya ta kudu.
Jamus na bukatar ta ci wasanta domin ta sami damar shiga zagaye na biyu a gasar amma ta kasa cimma wannan burin.
Wannan dai shi ne karo na farko a tarihin kasar Jamus da ta kasa kai wa zagaye na biyu a gasar cin kofin duniya..
Morocco, wadda ta sha kashi a hannun Jamus da ci 6-0 a wasan ta na farko kafin ta yi nasara a wasanni biyu a jere - za ta kara da Faransa a Adelaide a zagaye na biyu.
Colombia, wadda ta samu nasara a wasanninta biyu na farko ta kasance mai jan ragamar rukunin kuma za ta kara da Jamaica a birnin Melbourne a wasan dab da kusa da na ƙarshe ranar 8 ga watan Agusta.





