Shirin Rasha na daukar sabbin sojoji ba lalle ya yi tasiri ba - Birtaniya

Sabbin sojojin Rasha

Asalin hoton, EPA

An wallafa

Ma’aikatar tsaron Birtaniya ta ce shirin da Rasha take yi na kara yawan sojojinta ba lalle ba ne ya yi wani tasiri a yakin Ukraine.

 A kwanan nan Shugaban Rasahar Vladimir Putin ya sanya hannu a wata doka ta kara yawan dakarun kasar zuwa sama da miliyan 1.15, karin da zai kunshi  sojoji dubu 137 ke nan.

Sai dai Ma’ikatar Tsaron ta Birtaniya ta ce  wannan kari ba lalle ba ne ya yi wani tasiri ta wani bangare saboda asarar da Rashar ke yi ta sojanta.

Akwai rahotannin da ke cewa masu daukar sojin na ziyartar gidajen yari inda suke yi wa fursunoni alkawarin sakinsu tare da ba su kudi idan za su shiga aikin na soja.

A yanzu dai an takaita yawan sojojin Rasha zuwa sama da miliyan daya da kuma ma’aikata farar hula dubu 900 a rundunoninta.

 A lokacin daya daga cikin bayanan da take bayarwa a kan yakin na Ukraine akai-akai, ma’aikatar tsaron ta Birtaniya ta ce ba a kai ga sanin ko karin sojojin da Rashar za ta yi za ta yi ne ta hanyar daukar ‘yan sa-kai ba ko kuma ta hanyar tilastawa mutane shiga aikin.

 Ko ma dai ta yaya ne in ji sanarwar ta Birtaniya ba lalle ba ne shirin ya yi tasiri, saboda a cewarta Rasha ta rasa dubban sojojinta.

 Kuma ‘yan sa-kai kadan ne ke shiga, Sannan duk wadanda za a tilasta wa shiga sojin ba su da kwarewar da za su yi yaki da za su je yaki a wajen yankin Rasha, in ji sanarwar.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Jami’an kasashen yamma sun ce tun bayan da Rasha ta mamayi Ukraine wata shida da ya wuce an kashe ko raunata sojoji dubu 70 zuwa 80.

 Rasha ta shirya yakar Ukraine ne tsawon wani dan lokaci, lokacin da ta mamayi makwabciyar tata a watan Fabrairu, amma irin tirjiyar da ta gamu da ita daga Ukraine din abin ya hana ta samun cigaba.

Filin dagar yana naN yadda yake ba a  matsawa sosai.

 A yanzu dai ana iya tilasta wa mazaje ‘yan Rasha da ke tsakanin shekara 18 zuwa 27 shiga aikin soji.

Kodayake yawanci suna kauce wa shiga ko kuma rage yawan shekrun da za su yi wannan aiki yawanci da shekara daya ta hanyar kaucewa shigar a dalilai na rashin koshin lafiya ko kuma tafiya karatun gaba da sakandire.

 A halin da ake ciki kuma Ukraine ta zargi Rashar da kara harba makamai kusa da tashar nukiliya ta Zaporizhzhia  a cikin sa’a 24 da ta gabata.

Amma kuma Rashar ta mayar da martani da cewa sojojin Ukraine din ne ke harba makaman.

Shugaban tashar nukiliyar ta Ukraine, wadda Rasha ta karbe iko da ita, ya yi gargadin cewa za iya samun bullar turirin nukiliya idan har wani makami ya fada cikin makamashin da aka adana a kusa da na'urorin tashar.

Jami'ai a yankin da tashar take sun bayar da rhoton cewa ana harba makaman atilare na Rasha daga tashar zuwa garuruwan Ukraine da ke tsallaken kogin Dnipro.

Suma sojojin kasa na Ukraine a jiya Lahadi sun harba makamai masu linzami a garin Nova Kakhovka da ke hannun Rasha a yankin Kherson.

Wani babban jami'in Ukraine a yankin, Serhiy Khlan, ya ce dakarun rasha na amfani da tashar a matsayin wani snsanin soji.

BBC ba ta iya tantance ikirarin da kowane daga cikin bangarorin biyu ke yi ba.