Mutuwar Sarauniya Elizabeth II: An kafa sabuwar masarauta

Jim kadan bayan mutuwar Sarauniya , sai Yarima Charles ya dare karagar mulki.
Birtaniya na da sabon Sarki da shugaban kasa. Haka sauran kasashe 15 da suka hada da Austiraliya da New Zealand, wadanda su ma sarautar Birtaniya ke jan ragamar shugabancinsu.
Tsawon zamanin mulkin Sarauniya Elizabeth II ya kawo karshe ne bayan mutuwarta.
A wannan lokacin da zarar ta mutu za a mika ragamar mulki ba tare da wani biki ba ga babban danta, mai gadonta, tsohon Yarima na Wales. Wannan shi ne tsarin gadon sarautar gargajiya.
Doka ta tsara salsalar gadon sarauta tun daga karni na 17 da na 18.
A yanzu Yarima Charles dole ne ya zabi sunan da yake so a lakaba masa.
Ko zai yi mulki ne a matsayin Sarki Charles III, ko zai lakaba wa kansa wani sunan ne, alal misali ya zama Sarki George VII, don tunawa da kakansa, George VI, Sarkin da ya yi mulki a lokacin yakin Duniya na biyu?
Hawan sabon sarki karagar mulki zai kwarzanta da tabbatar da shi ne a Majalisar Hawan Karaga (ko kama rahgamar mulki - Accession Council) da ke Fadar St. James.

Asalin hoton, Getty Images
Wannan shi kawai babban taron da ke tattaro hamshakan 'yan majalisa 500, wadanda suka hada manyan ministocin gwamnati na da, da masu ci (a halin yanzu) don su tattauna.
Bayan an kammala taron Majalisar Hawan Karaga, sai a yi sanarwa a farfajiyar Fadar St. James ta bakin wani jami'i da ake yi wa lakabi da Garter King of Arms (tamkar Sarkin Yaki).
Bayan Karatun "tsararren Ikirarin" sai harbin bindiga sau 41 ya biyo baya a Hyde Park, sannan a sake yin wani harbin sau 62 a tulluwar Toliyar Landan.
Za a sake yin sanarwa a gidan wasa na 'Royal Exchange' da ke birnin Landan, a kofar shiga gidan sarauta na Edinburgh da ke Cardiff, sannan ko kuma a gidan sarauta na Hillsborough da ke Belfast.
Makura
Babu "rantsuwar kama ragama" a tsarin sarautar Birtaniya, sabanin na sauran shugabannin kasashe.
Mai sarauta kan yi rantsuwar kama ragamar mulki ne a Majami'ar Scotland a Majalisar Hawan Karaga, karkashin jagorancin Babban Shugaba a Cocin Ingila.

Asalin hoton, iStock
Aikin farko da sabon Sarki zai fara gudanarwa, shi ne jagorantar makokin mahaifiyarsa. Daga nan sai a yi gagarumin shiri.
Daukacin al'amuran dai, sukan kasance ne cikin kwanaki biyar da mutuwar Sarauniya, inda za a kewaya da makarar gawar sarauniya a keken dawaki ana ta harba bindiga daga rundunar baraden sarki, inda 'yan bindigar dawakan sarauta daga Fadar Buckingham za su isa Fadar Westminster.
A dakin taron Westminster za a ajiyeta tsawon kwana uku, ta yadda al'ummar gari za su samu damar yin ban kwana da ita cikin girmama.
Yin shiru
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Kwanaki 11 bayan mutuwarta, sai a yi wa Sarauniya jana'izar kasa Elizabeth II , wadda ake gudanarwa a Westminster Abbey.
Birtaniya ta dade ba ta yi jana'izar kasa ba, tun bayan zamanin yakin da aka yi wa Firaiminista Sa Winston Churchill a shekarar 1965.
Jana'izar Mahaifiyar Sarauniya (a shekarar 2002) da ta Diana da Yarima na Wales (a shekarar 1997), daukacinsu bukukuwa ne da aka saba yinsu, amma babu wadda aka dauke ta tamkar jana'izar kasa.
Daga nan sai a dauki makarar gawar Sarauniya ana kewayawa daga Fadar Westminster da harba bindigar ban-girma na kasa a kan keken dawaki, bisa tsarin Sojojin ruwan sarauta zuwa Westminster Abbey.
Daidai karfe 11:00 za a yi shiru na minti biyu don tunawa da mai sarauta mafi ban mamaki a tarihin Birtaniya.
Bayan jana'izar kasa, sai a dauki makarar gawar a kan titi zuwa gidan sarautar Windsor inda za a binne Sarauniya a farfajiyar Majami'ar St. George da ke gidan sarautar Windsor.
Za a binne ta a gefen mahaifiyarta da mahaifinta da ke kwance a gidan sarautar, inda aka binne sarakuna da wadanda suka zama sarauniya tsawon dubban shekaru.










