Abin da kuke son sani kan wasan Man City da Tottenham ranar Alhamis

Man City Tottenham

Asalin hoton, BBC Sport

An wallafa

Manchester City za ta karbi bakuncin Tottenham a kwantan wasan mako na bakwai a gasar Premier League da za su kece raini a Etihad.

City mai maki 39 tana ta biyun teburi da tazarar maki takwas tsakaninta da Arsenal ta daya, Tottenham ce ta biyar.

Dan wasan City mai tsaron baya, John Stones da Ruben Dias sun murmure daga jinya za su iya buga wasan na ranar Alhamis.

Shima Kevin de Bruyne zai iya buga fafatawar, bayan da aka bashi hutu ya kashe wata matsala ta kashin kansa.

Watakila dan wasan Tottenham, Rodrigo Bentancur ya buga wasan, bayan da ya warke daga raunin da ya ji a gasar cin kofin duniya a Qatar.

Watakila a fara fafatawar da Richarlison, wanda ya shiga sauyi a karawar da Arsenal ta ci Tottenham 2-0, yayin da Lucas Moura ke jinya.

Karawa tsakanin Manchester City da Tottenham

Manchester City ta yi rashin nasara a wasa hudu daga biyar a Premier League a hannun Tottenham a dokewar da aka yi mata fiye da a karawa 19 a baya a tsakaninsu.

Tottenham tare da Chelsea sun samu nasara a kan City sau 27 da suka fuskanci kungiyar a Premier League.

Watakila Tottenham ta zama ta farko da za ta doke City a wasa uku a jere a Lik karkashin Pep Guardiola.

Harry Kane

Asalin hoton, BBC Sport

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Manchester City

Watakila Manchester City ta yi wasa na uku ba tare da nasara ba karo na biyu tare da Pep Guardiola, bayan 2016 da suka yi hakan.

Wasa biyu a jere City ta yi rashin nasara a cikin watan Disambar 2018.

Wasa uku da aka ci City a bana kawo yanzu ya yi daidai da yawan wanda aka caskarata a bara da ta dauki kofin.

Guardiola ya yi rashin nasara a wasa uku baya daga biyar da ya fuskanci Antonio Conte, kociyan da ke bashi matsala ida suka hadu.

Erling Haaland ya yi wasa biyu a jere ba tare da cin kwallo ba a karon farko - ya taba fafatawa uku bai ci kwallo ba a bara tsakanin Maris zuwa Afirilu a Borussia Dortmund.

Jack Grealish ya ci kwallo daya ya kuma bayar da uku aka zura a raga, tun bayan kammala gasar kofin duniya.

Tottenham Hotspur

Tottenham na fatan cin wasa biyu a waje a jere a bana a karon farko.

Kungiyar tasha kashi a wasa hudu da ta yi da wadanda ke samanta a teburi a gasar Premier League a kakar nan.

An ci Tottenham kwallaye da yawa a karawa 11 a Premier League a bana, Bournemouth ce mai sakamako mafi muni.

Harry Kane na bukatar kwallo daya domin yin kan-kan-kan da Jimmy Greaves, mai tarihin ci wa Tottenham kwallo 266 a dukkan fafatawa.

Saura kwallo daya Kane zai ci ya zama na uku a jerin wadanda suka zura 200 a Premier League, bayan bajintar Alan Shearer da kuma Wayne Rooney.