Abin da ya kamata ku sani kan wasan Barca da Valladolid

Barcelona

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Ranar Lahadi Barcelona za ta karbi bakuncin Real Valladolid a wasan mako na uku a gasar La Liga da za su kara a Nou Camp.

Ranar 13 ga watan Agusta Barcelona ta fara wasan La Ligar na bana da Vallecano, inda ta tashi karawar 0-0.

Ranar 21 ga watan Agusta kungiyar Nou Camp ta ziyarci Real Sociedad a wasan mako na biyu, inda ta ci 4-1.

Barcelona za ta fafata da sabuwar kungiyar da ta hau gasar La Liga a kakar nan, wadda ta sha kashi a gida da ci 3-0 a hannun Villareal ranar wasanta na farko.

Ranar 19 ga watan Agusta, Valladolid ta je gidan Sevilla ta tashi 1-1 a wasan mako na biyu a babbar gasar tamaula ta Sifaniya.

Labari daga kungiyar Barcelona

Ba wani dan wasa da ya ji sabon rauni, ba wanda yake da hukuncin dakatarwa, saboda haka Xavi yana da 'yan wasa a kasa da zai zaba ya darje.

Shin ko kun san?

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Barcelona ba ta yi rashin nasara ba a wasa 15 da ta kara da Valladolid, inda ta ci 14 daga ciki da canjaras daya.

Tun daga kakar 2008/09 ta zura kwallo 40 a ragar Valladolid, ita ce kungiyar da ta zazzagawa da yawa tun daga lokacin.

Barcelona na bukatar cin kwallo a wasan nan, bayan da ta kasa zurawa a raga a wasa biyu baya a gida - rabon da ta yi uku ba tare da cin kwallo ba a gida tun 1980.

To sai dai Valladolid ta buga karawa 11 a waje a bayan nan ba tare da yin nasara ba, watakila ta kara shan kashi a hannun Barcelona.

Wasan karshe da suka kara a tsakaninsu

Kakar 2020/2021

La Liga ranar Litinin 5 ga watan Afirilun 2021 

Barcelona 1 - 0 Valladolid           

La Liga Talata 22 ga watan Disambar 2020  

Valladolid 0 - 3 Barcelona           

Idan har Gavi ya buga wasan zai zama dan kwallon da aka haifa a 2003 da zai yi wa Barcelona karawa ta 50. 

Kociyan Valladolid, Pacheta ya fuskanci Barcelona sau12 a matakin dan kwallo, bai yi nasara ba - a matakin koci a Huesca bai yi nasara a haduwa dayan da ya yi da Barcelona ba.

Alexia za ta gabatar da kyautar da ta lashe a Turai

 

Alexia Putella

Asalin hoton, Getty Images

Kafin a fara wasan kyaftin din kungiyar Barcelona ta mata, Alexia Putella za ta gabatar da kyautar da ta lashe a Istambul a gaban magoya baya a Nou Camp.

Ita ce aka zaba gwarzuwar 'yan kwallon kafa a nahiyar Turai ta bana ta kuma zama ta biyu da ta karbi kyautar karo biyu a jere a tarihi,

Sai dai 'yar wasan na jinya mai tsawo, bayan raunin da ta yi a watan Yuli.