Uefa ta sanar da fitattun ƴan wasa 11 na Euro 2024

Asalin hoton, Getty Images
Hukumar ƙwallon kafa ta Turai, Uefa ta sanar da ƴan wasa 11 da ba kamarsu a gasar cin kofin nahiyar Turai, wato Euro 2024.
Cikin ƴan wasa 11 da aka fitar guda shida daga tawagar Sifaniya suke har da matashin ɗan ƙwallo Lamine Yamal.
Ɗan wasa ɗaya ne daga Ingila shi ne Kyle Walker, wanda karo na biyu a jere yana shiga jerin fitattu 11 na Euro, bayan gasar da aka yi a 2021.
Ranar Lahadi Sifaniya ta lashe Euro 2024, bayan da ta doke Ingila 2-1 a birnin Berlin, kuma na hudu da ta lashe a tarihi.
Ba tawagar da ta kai Sifaniya yawan ɗaukar kofin nahiyar Turai, mai biye da ita uku ta ɗauka ita ce Jamus, sai Faransa da Italiya da kowacce keda biyu.
UEFA Euro 2024 fitattun ƴan wasa 11: Mike Maignan (France); Kyle Walker (England), Manuel Akanji (Switzerland), William Saliba (France), Marc Cucurella (Spain); Daniel Olmo (Spain), Rodri (Spain), Fabian Ruiz (Spain); Lamine Yamal (Spain), Jamal Musiala (Germany), Nico Williams (Spain)





