Majalisar dattijan Faransa ta amince da bai wa mata ƴancin zubar da ciki

Asalin hoton, AFP
Majalisar dattijai a Faransa ta amince da wani ƙudirin doka da bayar da damar amincewa da zubar da ciki a matsayin ƴancin ɗan Adam da kundin mulkin ƙasa ya yi tanadi.
Duk da cewa zubar da ciki haram ne a Faransa, shugaba Macron ya yi alƙawarin mayar da shi ƴancin ɗan Adam.
Ƴan majalisar Faransar sun amince da ƙudirin dokar ne, bayan kafa hujja da ƙasashe irin su Amurka, inda mace bata da ƴancin yanke hukunci kan ko zata zubar da ciki ko kuma za ta haife shi.
A watan da ya gabata ma majalisar wakilai ta amince da ƙudirin.
Da yake jawabi bayan sanatocin sun kammala kaɗa ƙuri’a game da ƙudirin, ministan shari’a ne Fransa ya ce Éric Dupond-Moretti ya ce wannan nasara ce mai muhimmancin gaske.
Ya ce: "Cikin daren nan, majalisar dattijai ta buɗe sabon babi a ƙoƙarin tabbatar da ƴancin mata. Za mu zamo ƙasa ta farko da ta sanya batun baiwa mata ƴancin kula jikinsu, a cikin kundin mulkin ƙasa. Wannan ba ƙaramin tarihi bane. Kuma wannan abu ne da ke ƙara jaddada yadda mata ke da ƴanci a ƙasar."
A ranar litinin majaisar za ta yi wani zaman haɗin gwiwa, inda ake sa ran ta amince da ƙudirin dokar.
Yanzu dai Faransa ta kama hanyar zama ƙasa ta farko a duniya da ta sanya ƴancin zubar da ciki ga mata, a cikin kundin mulkin ta,












