Bayern Munich na son Eze, De Bruyne na shawara kan Napoli

Asalin hoton, Getty Images
Bayern Munich na shawara kan ɗan wasan tsakiya a Crystal Palace da Ingila, Eberechi Eze mai shekara 26, bayan rashin nasara kan ɗan wasan Liverpool da Jamus, Florian Wirtz, mai shekara 22. (Mirror)
Liverpool ta gabatar da tayin sama da £320,000 kowanne mako kan ɗan wasan Bayer Leverkusen, Wirtz a kokarin ganin sun daidaita kan lokaci. (Sky Sports Switzerland - in French)
Zakarar Bundesliga, Bayern Munich ta nuna kwaɗayinta kan ɗan wasan Brighton da Japan, Kaoru Mitoma mai shekara 28, da kuma mai taka leda a AC Milan, Rafael Leao mai shekara 25. (Mirror)
Ɗan wasan tsakiya a Manchester City Kevin de Bruyne, mai shekara 33, na gab da yanke hukunci kan tafiyarsa ƙungiyar Napoli ta Serie A nan da mako biyu. (Mail)
Liverpool da Newcastle na gwada ƙwanji kan ɗan wasan Brighton, mai shekara 23 daga Brazil, Joao Pedro. (Talksport)
Makomar ɗan wasan Ingila, Jack Grealish a Manchester City na cikin rashin tabbas bayan matashin mai shekara 29 ya fice daga filin wasa a karawarsu ta karshe da Fulham. (Telegraph - subscription required)
Kocin Manchester United, Ruben Amorim ya sanar da 'yan wasan sa cewa zai ci gaba da zama a Old Trafford. (Athletic - subscription required)
Kyaftin Bruno Fernandes mai shekara 30 daga Portugal, na ɗaya daga cikin 'yan wasa shida na ƙungiyar Manchester United da za su sauya sheka. (Football Insider)
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Ɗan wasan Denmark, Rasmus Hojlund mai shekara 22 na kokarin yanke hukunci kan makomarsa yayin da Manchester United ke gabatar da tayinta. (GiveMeSport)
Inter Milan na son cimma yarjejeniya da ɗan wasan tsakiya a Real Madrid mai shekara 39, Luka Modric, bayan ɗan wasan na Croatia ya tabbatar da barin ƙungiyarsa a wannan kaka. (Fichajes - in Spanish)
Nottingham Forest na duba yiwuwar saye ɗan wasan Liverpool mai shekara 22, Jarell Quansah. (Football Insider)
Ɗan wasan baya a Manchester United Victor Lindelof zai bar ƙungiyar da zarar kwantiraginsa ya kare a karshen kaka. (Fabrizio Romano)
Newcastle na fafatawa da Napoli da Juvestuns da Roma a cinikin ɗan wasan Atletico Madrid da Argentina, Nahuel Molina, mai shekara 27. (Marca, via Sportwitness)
Galatasaray ta gabatar da tayi kan ɗan wasan Jamus, Leroy Sane, mai shekara 29, da kwantiraginsa a Bayern Munich ya kare a wannan kaka, yayin da yake samun tayi daga Napoli da sauran ƙungiyoyin Firimiya. (Sky Germany - in German)










