Man Utd ta yi wa Garnacho farashi, Arnold na daf da rattaba hannu a Madrid

Asalin hoton, OTHERS
Manchester United ta bayyana farashin Alejandro Garnacho, kungiyoyin Premier biyu na zawarcin Nicolas Pepe, makomar Leroy Sane na Bayern Munich na cikin shakku.
Manchester United ta shaida wa Chelsea cewa za ta biya fam miliyan 65 don siyan dan wasan gabanta dan Argentina Alejandro Garnacho, mai shekara 20 a bana. (Star)
Everton da Wolves suna sha'awar sayen tsohon dan wasan Arsenal Nicolas Pepe, mai shekara 29, dan kasar Ivory Coast din kwantiraginsa a Villarreal a bazara. (Foot Mercato)
Dan wasan gefe na Jamus Leroy Sane, mai shekara 29, ya sauya wakilinsa, wanda abun da ya janyo ayar tambaya kan makomarsa a Bayern Munich da kuma tsawaita kwantiraginsa da aka kusa cimma yarjejeniya. (Sky Sports Germany)
Liverpool na shirin kashe makudan kudade a bazara don siyan sabon dan wasan baya na hagu da na tsakiya da kuma dan wasan gaba. (Talksport)
Chelsea na shirin tattaunawa da dan wasan tsakiya na Ecuador Moises Caicedo, mai shekara 23, kan sabon kwantaragi a bazara a matsayin ladan kokarin da ya nuna a bana. (Telegraph)
Dan wasan bayan Liverpool da ke shirin barin kungiyar Trent Alexander-Arnold na shirin rattaba hannu kan kwantiragin shekaru shida da Real Madrid wanda zai fara aiki daga ranar 1 ga watan Yuli. (The Athletic)
Alexander-Arnold, mai shekara 26, ya yi watsi da tayin karin albashin da aka yi masa na ci gaba da zama a Liverpool bayan karshen kakar wasa ta bana. (ESPN)
Manchester United da West Ham na neman golan Southampton da Ingila Aaron Ramsdale, mai shekara 26. (Mirror)
Kocin Fulham Marco Silva da kocin Nottingham Forest Nuno Espirito Santo na daga cikin 'yan takarar da kulob din Al-Hilal na Saudi Pro League ke zawarci. (Talksport)
Aston Villa na zawarcin golan Real Madrid da Ukraine Andriy Lunin, mai shekara 26, yayin da golan Argentina Emiliano Martinez, mai shekara 32, ake ci gaba da alakanta shi da barin kungiyar a bazara. (Birmingham Mail)











