Harry Kane zai zauna a Bayern Munich, Watakil Rodrygo ya bar Madrid

.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Harry Kane
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Dan wasan gaba na Brazil, Rodrygo, 24, na duba yiwuwar barin kungiyar Real Madrid idan an bude kasuwar saye da saida 'yan wasa a lokacin bazara.(Radio Marca)

Manchester United da Juventus na zawarcin dan wasan tsakiya na Brazil Ederson mai shekaru 25, daga Atalanta. (Tuttosport)

Ana alakanta mai kai hari na Ingila Harry Kane, da zai koma kungiyar Premier League sai dai dan wasan mai shekara 31, na son kara shekara guda a Bayern Munich . (Talksport)

Kungiyoyin kwallon kafa na Saudiyya, na zawarcin ,mai tsaron ragar Argentina, da ke taka leda a Aston Villa, Emiliano Martinez mai shekara 33, da dan wasan tsakiya na Jamaica, Leon Bailey, mai shekara 21.(Telegraph)

Bayern Munich na ganin ta na da kyakkyawar damar dauko dan wasan tsakiya na Jamus, Florian Wirtz daga Bayer Leverkusen, wanda ke kokarin saida dan wasa mai shekara 21 ga wani kulub din idan ya damu lallai sai ya bar kungiyar. (Sky Sports)

Tsohon kocin Manchester United Erik ten Hag, na cikin jerin wadanda kungiyar Bayer Leverkusen ke son maye gurbin Xabi Alonso da su, wanda ake rade-radin zai tafi Real Madrid domin maye gurbin Carlo Ancelotti. (Sky Sports Germany)

Dan wasan Ingila, Harvey Elliott, 22, na fadi tashin yin wasa a wannan kakar a Liverpool, amma dai ya na son ci gaba da zama da kwatar wa kan shi 'yanci a kungiyar.(Liverpool Echo)

Everton na cikin kulub din da ke zawarcin mai kai hari na Ipswich Town,Liam Delap mai shekara 22, an yi amanna farashin dan wasan ya kai fam miliyan 30. A bangare guda kuma babu tabbacin ko dan wasan gaba na Ingila Dominic Calvert-Lewin, 28, sai rattaba hannu kan sabon kwantiragin da ya wuce kakar nan. (The i Paper)

Mai tsaron baya na Koriya ta Kudu, Kim Min-jae ya ce ya na fatan zai ci gaba da zama a kungiyar Bayern Munich, duk da cewa kulub din na Jamus na nuna alamun saida dan wasan mai shekara 28, da zarar wani kulub ya nuna sha'awar sayan shi.(Sport Bild)

Dan wasan gaba na Faransa, Enzo Kana-Biyik, 18, na gab da kammala yarjejeniyar komawa taka leda kungiyar Manchester United, daga kungiyar Le Havre da ya ke takawa leda. (Manchester Evening News)

Tsohon kocin Wolves da West Ham Julen Lopetegui, ya rattaba hannu kan yarjejeniyar da za ta bashi damar zama kociyan Qatar, ana sa ran yarjejeniyar za ta kai watan Yunin shekarar 2027. (Fabrizio Romano)