Arsenal na son Rodrygo, Man United ta shiga neman Araujo da Mbeumo

Bryan Mbeumo na jan hankalin Manchester United, Rodrygo zai iya barin Real Madrid, Manchester City na son Morgan Gibbs-White Real Madrid na zawarcin William Saliba.
Manchester United ta shirya tsaf domin shiga takarar neman dan wasan gaban Kamaru Bryan Mbeumo, mai shekara 25, da aka kimanta kan fan miliyan 60 daga Brentford a wannan bazarar. (Telegraph)
Arsenal ta nemi sayen dan wasan gaban Brazil Rodrygo daga Real Madrid, yayin da Manchester City kuma ke zawarcin dan wasan mai shekaru 24. (Relevo)
Har ila yau Manchester City na shirin ci gaba da neman kulla yarjejeniya da Nottingham Forest kan dan wasan tsakiyar Ingila Morgan Gibbs-White, mai shekara 25. (Fabrizio Romano)
Arsenal da Aston Villa na zawarcin dan wasan Juventus Dusan Vlahovic, mai shekara 25, inda ake sa ran kulob din na Seria A zai nemi dan wasan na Serbia a kan farashin fan miliyan 42. (Fichajes)
Everton ta shirya yin hamayya da Manchester United don siyan dan wasan Ipswich Liam Delap, mai shekara 22. (Teamtalk)
Manchester United ta shirya yin tayin siyan dan wasan bayan Barcelona da Uruguay Ronald Araujo, mai shekara 26, idan ta samu tikitin shiga gasar zakarun Turai. (Football365)
Leeds ta sanya dan wasan bayan Marseille na Argentina, Leonardo Balerdi, mai shekara 26, cikin wadanda take son siya a bazara. (Sun)
Real Madrid ta aike da wakilanta domin kallon dan wasan bayan Bournemouth dan kasar Sipaniya Dean Huijsen, mai shekara 20, da dan wasan bayan kasar Hungary Milos Kerkez, mai shekara 21, a wasan da suka doke Arsenal a ranar Asabar. (TBR Football)
Haka kuma kungiyar na zawarcin dan wasan bayan Arsenal da Faransa William Saliba, mai shekara 24, wanda kwantiraginsa da Gunners zai kai har 2027. (L'Equipe)
West Brom na son kocin Tottenham dan kasar Ingila Ryan Mason, mai shekara 33, ya zama sabon kocinta. (Sun)
Kocin Fulham dan kasar Portugal, Marco Silva, mai shekara 47, na neman maye gurbin Ange Postecoglou a Tottenham idan an kori dan kasar Australia din mai shekaru 59 bayan rashin nasarar kungiyar. (Football Insider)











