Nkunku zai bar Chelsea, Aston Villa na iya fuskantar cikas kan Rashford

.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Rashford
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Dan wasan gaba na Faransa, Christopher Nkunku, 27, ya yanke shawarar barin kulub din Chelsea da kakar nan. (Sky Sports Germany)

Mai tsaron baya na Ukraine Oleksandr Zinchenko, 28, ka iya barin Arsenal a kakar nan, inda kungiyar Borussia Dortmund ke son dan wasan. (Football Insider)

Dan wasan tsakiya na Amurka, Weston McKennie, 26, ya cimma matsaya da Juventus ya ci gaba da zama a kungiyar har zuwa shekarar 2028. (Fabrizio Romano)

Manchester United, da Chelsea da Tottenham Hotspur na daga cikin kungiyoyin da ke son dauko dan wasan baya na, Bournemout, Dean Huijsen mai shekara 20. (CaughtOffside)

Aston Villa ka iya fuskantar tangarda wajen dauko dan wasan gaba na Ingila, Marcus Rashford, 27, daga Manchester United idan ba su kai bantensu a gasar Champions League. (Football Insider)

Magoya bayan Aston Villa sun yi dandazo, domin ganin dan wasan gaba na Porto da Sifaniya Samu Aghehowa, 20, gabannin daukar shi da kulub din zai yi a kakar nan. (Record , externalvia Sports Witness)

Everton na tababar sake maido tsohon mai kai hari na kungiyar Richarlison, 27, inda kungiyar da ya ke takawa leda watoTottenham Hotspur ta amince ta karbi fam miliyan 40 kan dan wasan. (GiveMeSport)

Real Madrid na duba yiwuwar dauko dan wasan baya na Real Sociedad Jon Aramburu, 22 a lokacin bazara. (Fichajes)

Leeds United sun kara dan wasan gaba na AZ, Troy Parrott, 23, cikin jerin sabbin 'yan wasan da za su dauko, bayan ci gaban da uka samu a Premier League. (TeamTalk)

Fiorentina na gab da tsawaita kwantiragin mai tsaron baya, Pietro Comuzzo mai shekara 20, daidai lokacin da kulub din Napoli ke zawarcin dan wasan. (Tuttomercato)

Liverpool ka iya daukar matakin bazata kan dan wasan gaba na Real Madrid Rodrygo, 24, inda dan Brazil din ya amince da barin Safiniya. (GiveMeSport)

Ajax na son saida mai tsaron gida na Netherlands, Jorrel Hato, ya yin da idon matashin dan wasan mai shekara 19, ke Chelsea. (Kick-off podcast)