Abubuwan da suka sa ƴan Najeriya farin ciki a 2024

Asalin hoton, State House
A yayin da shekarar 2024 ke bankwana, shekarar ta kasance mai cike da ƙalubale a Najeriya, daga matsalar rashin tsaro zuwa matsin tattalin arziki.
Sai dai duk da cewa ko a rahoton ƙasashen da ƴan ƙasarsu suka fi farin ciki a duniya Najeriya ba ta cikin 10 ko 20 na farko, akwai abubuwa da dama da suka faru a shekarar waɗanda aƙalla suka sanya wasu ƴan ƙasar farin ciki.
Ga wasu daga cikin abubuwan da muka zaƙulo.
Ƙarin albashi mafi ƙanƙanta

Asalin hoton, Reuters
A ranar 18 ga watan Yuli ne shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya amince da ƙarin albashi mafi ƙanƙanta zuwa naira 70,000 ga ma'aikatan ƙasar, inda ya yi alƙawarin za a rinƙa nazari kan mafi ƙanƙantar albashin duk bayan shekara uku.
Kafin wannan ƙarin dai mafi ƙanƙantar albashi a ƙasar naira dubu 30 ne wanda ƙungiyoyin ƙwadago suka nemi a ƙara zuwa sama da naira 400,000 saboda hauhawar farashin kaya da ake fama da ita.
An dai yi ta kai ruwa rana tsakanin ƙungiyoyin ma'aikata da ita gwamnatin gabanin cimma matsaya.
Har sai da ta kai ga cewa ƙungiyar ƙwadago ta NLC da TUC sun kira yajin aiki tare da tsayar da al'amura cak a farkon-farkon shekarar ta 2024.
Yanzu dai gwamnatin tarayya a ƙasar ta soma biyan mafi ƙanƙantar albashin ga ma'aikatanta, kuma jihohi da dama a ƙasar ma sun bi sawun gwamnatin.
Matatar man fetur ta Dangote

Asalin hoton, ALIKO ƊANGOTE/X
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
A ranar 13 ga watan Janairu, matatar man fetur ta Aliko Dangote - wadda aka kashe kimanin dala biliyan 20 - ta fara aiki.
Duk da cewa Najeriya na ɗaya daga cikin ƙasashen duniya da suka fi samar da ɗanyen man fetur, a shekarun baya-bayan nan, ƙasar na fuskantar ƙarancin man fetur da kuma hauhawar farashinsa.
Saboda haka nan fara aikin matatar Dangote ya sanya ƴan Najeriya da dama farin ciki tare da kyakkyawar fatan cewa za ta kawo sauƙi ga wahalhalun da suke sha a ɓangaren man fetur.
Wasu ma sun yi tunanin cewa samuwar matatar ta Dangote za ta sanya farashin litar man fetur - wanda ta yi tashin gwauron zabi tun bayan cire tallafin man fetur - zai yi ƙasa.
Sai dai taƙaddamar da ta ɓarke tsakanin Dangote da kamfanin man fetur na Najeriya NNPCL ta sarayar da guyawun al'ummar ƙasar.
NNPCL ya lafta zarge-zarge a kan matatar Ɗangote - kamar rashin samar da ingantaccen man fetur da kuma ƙoƙarin yin kaka-gida a harkar.
Lamarin ya kai ga cewa Dangote ya yi wa NNPCL tayin sayen matatar tasa, sannan kuma ya yi zargin cewa kamfanin ya gaza cimma alƙawarin da ya yi tun farko na sayen kashi 20 cikin 100 sannan kuma ba ya sayar masa da ɗanyen man fetur a kuɗin naira kamar yadda aka yi yarjejeniya tun da farko.
Kashe gawurtattun ƴan bindiga

Asalin hoton, Others
- Halilu Sububu
A cikin watan Satumba ne sojojin Najeriya suka sami nasarar hallaka ƙasurgumin ɗan bindiga da suka daɗe su na nema ruwa a jallo wato Kachalla Halilu Sububu, wanda ya addabi yankin arewa maso yammacin ƙasar.
Sanarwar da rundunar sojin ta fitar game da kisan Halilu ta ce dakarun sun kashe shi ne tare da wasu mutum 30 a lokacin.
- Buharin Yadi
Sojojin Najeriya sun sun ce sun kashe wani ƙasurgumin ɗan bindiga da ya addabi wasu yankunan arewa maso yammacin ƙasar mai suna Kachalla Buhari Alhaji Halidu da aka fi sani da Buharin Yadi da wasu yaransa fiye da 30.
Ƙasurgumin ɗan bindigar ya yi ƙaurin suna wajen kai hare-haren satar shanu da safarar makamai, da tashe-tashen hankula a jihohin arewacin ƙasar da dama.
- Ɗangote
A watan Yulin 2024 ne jami'an tsaron Najeriya suka hallaka shi yayin wata musayar wuta a dajin Dumburun da ke jihar Katsina.
- Boderi Isyaku
Boderi Isiyaku ne dai mutumin da ya yi garkuwa da ɗalibai 39 daga kwalejin gwamnatin tarayya ta koyon aikin gona. Kuma sojoji sun samu nasarar hallaka shi ne a watan Agustan 2024.
- Dogo Rabe
Rabe ya yi ƙaurin suna a jihar Zamfara inda ya daɗe yana addabar al'ummar jihar. To sai dai ya haɗu da gamonsa ne a watan Satumban 2024 a yayin wani samame da sojojin suka kai a maboyarsa da sassafe.
Ademola Lookman - gwarzon ɗan ƙwallon Afirka

Asalin hoton, Getty Images
A ranar 16 ga watan Disamba, ɗan wasan ƙwallon ƙafa na tawagar Super Eagles ta Najeriya da ƙungiyar Atalanta ta Italiya, Ademola Lookman ya lashe kyautar ɗan ƙwallon ƙafa na Afirka.
Ɗan wasan ya doke fitattun zaratan ƴan wasa irin Achraf Hakimi na Morocco da Simon Adingra na tawagar Ivory Coast da ƙungiyar Brighton & Hove Albion ta Ingila da Ruto Williams na Afirka ta Kudu da Serhou Guirassy na ƙasar Guinea da ƙungiyar Dortmund ta Jamus domin lashe kyautar.










