Pierre-Emerick Aubameyang ya yi amai ya lashe

Asalin hoton, Getty Images
Dan kwallon Chelsea, Pierre-Emerick Aubameyang zai koma buga wa tawagar Gabon wasanni, shekara daya bayan yin ritaya.
Mai shekara 33 ya yi ritaya a Mayun 2022 a matakin wanda ke kan gaba a ci wa kasar kwallaye, bayan zura 28 a raga a wasa 68.
Tsohon dan wasan Arsenal ya ce zai koma buga wa Gabon wasanni, bayan da shugaban kasar, Ali Bongo Ondimba ya umarce shi da yin hakan.
Gabon, wadda tsohon mai tsaron bayanta, Patrice Neveu ke jan ragama tana ta daya a rukunin da take a neman shiga gasar kofin Afirka na badi.
Kasar za ta iya samun gurbin shiga gasar da Ivory Coast za ta karbi bakunci a 2024, idan ta ci Jamhuriyar Congo a cikin Yuni, duk da wasa daya zai rage bayan karawar.
Aubameyang ya fara yi wa Gabon tamaula a 2009, wanda ya fuskanci kalubale karo da yawa - ciki har da karbe kyaftin din Arsenal a Disambar 2021.
Daga nan ya koma taka leda a Barcelona a watan Janairu daga Gunners.
Ana alakanta shi da zai koma Camp Nou, kungiyar da ya fara yi mata tamaula a 2022-2023.
Barcelona ta sanar cewar za ta bai wa Aubameyang lambar zinaren lashe La Liga na bana, duk da minti takwas ya buga mata daga nan ya koma Chelsea.
Aubameyang ya koma buga Premier League a Arsenal daga Borussia Dortmund a 2018 karkashin Arsene Wenger, wanda ya ci kwallo 92 a wasa 142 a Gunners.











