Barazanar da ma'aikatan kula da tsofaffi 'yan kasashen waje ke fuskanta a Birtaniya

Blurred care worker and resident at Addison Court care home
Bayanan hoto, Wani ma'aikaci tare da mazaunin gidan kula da tsofaffi na Addison Court da ke kusa da Newcastle
    • Marubuci, BBC Panorama
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Reporting team
  • An wallafa

Ma’aikatan gidajen kula da masu rauni sun shaida wa BBC cewa kamfanin da ya kawo su Birtaniya ya yi amfani da su kuma a halin yanzu ya makalar da su.

Ma'aikata a Prestwick Care sun shaida wa wakilin shirin Panorama na BBC da ya ɓatar da kama cewa suna da yakinin cewa kwantiraginsu ya hana su fita.

Binciken BBC ya kuma yi la'akari da matsalar karancin ma'aikata, wadda kwararru a bangaren kiwon lafiya suka ce yana jefa mazauna gidajen cikin hadari.

Gidan Prestwick Care ya musanta duk wani zargin aikata ba daidai ba.

Wani dan jaridan Panorama ya sauya kama kuma ya karbi aiki a matsayin mai kula da mazauna gidan Addison Court da ke Ryton - daya daga cikin gidajen kulawa 15 a arewa maso gabashin Ingila mallakar Prestwick Care. Ya yi aiki a can daga watan Satumba zuwa Nuwamba na wannan shekara, bayan ya ji zarge-zarge daga kwararrun sashen kiwon lafiya game da yanayin gidajen.

Addison Court gida ne ga tsofoffi fiye da 50, wadanda ke biyan kimanin fan £1,100 kowanne mako. Kuddaden na fitowa ne daga ƙaramar hukuma ko NHS, ko kuma mazauna da danginsu.

Kamar gidajen kulawa da yawa a cikin Birtaniya, Addison Court ya dogara sosai kan ma'aikata daga kasashen ketare.

Exterior of Addison Court
Bayanan hoto, Addison Court daya ne daga cikin gidajen kulawa 15 a arewa maso gabashin Ingila mallakar Prestwick Care

Zuwa watan Satumban 2023, an ba da biza 140,000 ga ma'aikatan kiwon lafiya da kulawa na kasashen ketare don zuwa Burtaniya - fiye da ninki biyu na bara. Daga cikin waɗannan, an ba da biza 39,000 ga mutane daga Indiya.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Ma'aikatan jinya da ma'aikatan kulawa daga ketare sun cancanci samun bizar ƙwararrun ma'aikata. Wannan yana nufin cewa za su iya aiki a Burtaniya, amma suna bukatar masu daukar mai'aikata su dauki nauyin su.

Idan sun bar aikinsu, suna da kwanaki 60 don neman wani aiki da ya dace - in ba haka ba dole ne su koma kasarsu ta asali.

An nuna damuwa game da ikon da wannan ke bai wa masu daukar ma'aikata.

Andrew Wallis na wata kungiyar agaji ta Unseen ta yaki da muzgunawa ma'aikata ya ce "Idan kana kan karagar mulki a matsayin shugaba, to za ka iya daukar matakin tilastawa mutum iko."

Prestwick Care yana ɗaukar ma'aikata kusan 180 daga ƙasashen waje waɗanda ke cikin Burtaniya akan biza - kusan kashi ɗaya bisa uku na ma'aikatanta.

Wata ma’aikaciyar jinya 'yar kasar Indiya da ke wurin ta shaida wa dan jaridan cewa ba ta ji dadin aikinta ba, amma ta ji kamar ba za ta iya ajiye aikin ba, saboda kamfanin ne ya dauki nauyin bizar ta, kuma ta yi tunanin cewa ba ta da wani zabi.

Nurse at Addison Court complains about the pressure she is under
Bayanan hoto, Mai'aikaciyar jinya a Addison Court: "Ba zan iya tafiya kawai ba"

"Ba zan iya fita daga nan ba, da a gida na ke zan iya ajiye aiki na. Amma a nan, ba zan iya tafiya haka nan kawai ba," in ji ta.

Prestwick baya sassauta wa ma'aikatan jinya na ƙasashen waje waɗanda suka zaɓi barin kamfanin.

Ahmed (ba sunansa na ainihi ba), ya zo Burtaniya daga jihar Kerala ta kudancin Indiya a cikin 2018.

Lokacin da ya isa, an nemi ya sanya hannu kan kwangilar kama aiki. Kwangilar ta kunshe cewa idan ya bar kamfanin a cikin shekaru biyar, sai ya biya Prestwick Care sama da fam 4,000, wanda ya hada da kudin da kamfanin ya riga ya biya ga ma’aikatar cikin gida, da kuma kudaden da aka biya kan bizarsa.

Bisa ga ka'idojin da'a na Ma'aikatar Lafiya da Kula da Jama'a (DHSC), bai kamata ma'aikata su biya waɗannan kuɗaden ba.

Ahmed ya ce an gaya masa: "Idan ba ka son zama a nan kan wannan kwantiragin, za ka iya komawa Indiya."

Ya ce yana jin Prestwick Care na kokarin hana shi fita, amma duk da haka ya yi murabus bayan da aka ba shi babban mukami a wani gidan kulawa da wani kamfani ke gudanarwa.

Daga nan ne Prestwick Care ta fara shari’a akan Ahmed, inda ya ce kamfanin na bin shi bashin sama da fam 5,000.

Daga nan ya kira Bunty Malhotra, Shugaban Malhotra Group, wanda ke mallakar Prestwick Care. Ya ce wa Ahmed, "Abin da ka yi rashin mutunci ne da rashin ɗa'a kuma mai matukar muni."

An kuma shiada wa Ahmed cewa wani sharadi a cikin kwantiraginsa ya hana shi yin aiki a duk wani gidan kula da masu rauni na tsawon wata shida.

"Ahmed" in silhouette
Bayanan hoto, An shaida wa ''Ahmed'' cewa zai biya wadansu kudade idan har ya bar aiki a kamfanin

Liana Wood lauya ce. Ta ce babu wata kotu da za ta amince da wannan sharadin, kuma ta ce an makala shi ne kawai "don cimma manufar yi wa ma'aikatan jinya da manyan mataimakan kulawa dabaibayi a cikin halin da suke ciki".

Daga baya dai sabon kamfanin da yake yi wa aiki ya sasanta batun shari’ar Ahmed.

Andrew Wallis na Unseen ya ce shugabanni marasa gaskiya na amfani da daurawa ma'aikata basussuka a matsayin wata hanyar takura su.

Prestwick Care ya musanta cewa an tsara kwangilolinta ne don tsoratar da ma'aikatanta kuma ya ce yanzu yana nazarin sharuddan da suka shafi kudade a duk kwangilolin ma'aikata.

Ga wasu daga cikin ma’aikatan Addison Court, lamarin ya kara dagulewa ganin yadda suma sun biya kudin biza da ya kama daga fam 6,000 zuwa 10,000 ta hannun wani kamfanin daukar ma’aikata mai suna BGM Consulting.

Kudin bizar shekara uku bai kamata ya wuce £ 551 idan sun mika bukata kai tsaye a shafin Intanet na gwamnatin Burtaniya.

Ma'aikatar lafiya ta Birtaniya ta ce bai kamata kamfanoni su yi aiki da kamfanonin daukar ma'aikata da ke karban kudade a hannun masu neman aiki ba.

Darektan BGM, Sunil Thomas, ya ce kamfanin bai karbi wani kudi don daukar ma'aikatan kulawa a Birtaniya na, kuma ya yi ikirarin cewa duk wani kudin da aka biya zai kasance ga "wakilai" ne a Indiya da ke aiki ba tare da saninsa ba.

Prestwick Care ya ce yanzu ya dakatar da duk sabbin shirye-shirye da ke tsakanin kamfanin da BGM Consultancy.

Har ila yau, dan jaridar ya ji korofr-korofe kan yadda karancin ma'aikata ke shafar tsarin kulawa a Addison Court.

Babu ƙa'idodi kan adadin ma'aikatan da gidan kula da masu rauni ya kamata ya ɗauka. Prestwick Care ya ce a lokacin aikin dare (tsakanin karfe 20:00 da 08:00), ma’aikaciyar jinya za ta iya ba da cikakkiyar kulawa ga mazauna 54, saboda suna da wadanda ke tallafa musu, waɗanda wasunsu na iya ba da magunguna.

Sai dai wata ma’aikaciyar jinya ta hukumar da ta yi aikin dare ta shaida wa dan jaridan cewa, lamarin na da wahala, kuma wasu mazauna ba su samun magungunansu a kan lokaci.

Rashin bayar da magunguna a kan lokaci na iya haifar da mummunan sakamako ga wasu marasa lafiya, misali, allurar insulin ga masu ciwon suga, ko magungunan cutar Parkinson.

Night shift nurse seen in corridor
Bayanan hoto, Ma'aikatan jinya sun nuna damuwa game da rashin ma'aikata a lokutan aikin dare

Ma’aikacin jinyan ya ce ya taba kokarin tattaunawa kan damuwar lamarin daukar ma’aikata da Bunty Malhotra. Ya ce Mista Malhotra ya zage shi kuma ya yi watsi da bayanin da ya yi masa - batun da Mista Malhotra ya musanta.

Haka kuma sauran ma’aikatan Addison Court sun shaidawa dan jaridan da ya yi shigar burtu cewa an nuna damuwa game da karancin ma’aikata, amma hukumar gidan ba ta nuna kula kan lamarin ban.

Ma'aikatan kiwon lafiya na cikin gida sun bayyana damuwar ma'aikatan.

Wata likitan da ke da marasa lafiya a Addison Court, wanda ta nemi a sakaya sunanta, ta shaida wa Panorama cewa ta ga wani yanayi tare da wasu marasa lafiya ba sa samun magungunan su akan lokaci.

Ta ce ma’aikatan sun fahimci cewa ba a cika ba da isashen kula yadda ya kamata ba, amma suna ganin babu wani amfanin gabatar da damuwarsu ga hukumar, saboda ko dai su yi yunkurin jingina masu laifi ko kuma su yi kokarin yin watsi da batun baki daya.

Manajan Addison Court ta ce ba gaskiya ba ne cewa ta kasa bincikar koke-koke, kuma ta ce tana da kyakkyawar alaka da ma'aikatan gidan.

Ma'aikaciyar NHS Katy Maughan ta ziyarci gidan sau ɗaya a mako har zuwa bara. Ta ce ma’aikatan jinya da ta yi magana da su ba su jin dadin aikin, amma suna ganin ceawa ba za su iya bari ba.

Ta yi tunanin cewa ma’aikatan ba su iya nuna damuwarsu saboda ba sa so su tayar da hankalin kamfanin wanda zai iya sanadiyar barinsu kasar.

Katy Maughan
Bayanan hoto, Ma'aikaciyar NHS Katy Maughan ta yi bayanin matsaloli 33 game da Addison Court.

Ms Maughan ta ce ta damu matuka game da wasu mazauna gidan har ta yi gargadi kan batutuwa 33 cikin shekaru biyu ga karamar hukumar Gateshead.

Ɗaya daga cikin waɗannan batutuwan sh ne game da wani mazaunin da ta ce ya mutu bayan an bar shi na tsawon sa'o'i 72 tare da ya ke fama da rshin yin bayan gida. Ta yi imanin cewa lamari ne da za a iya gujewa.

"Ya kamata su (ma'aikatan) su kasance suna magana da likita kuma suna cewa, duba, har yanzu bai samu yin bayan gidan ba, kuma ya kamata su kasance suna samun shawarwarin likita. Wannan sakaci ne."

Majalisar Gateshead ta gaya wa Panorama ba ta iya bayyana sakamakon abubuwan da ke tattare da batutuwan da aka lissafa saboda zai ƙunshi fitar da bayanan sirri masu mahimmanci. Ta ce an mayar da martani kan kowane batu kuma "an gudanar da ita bisa ga maslahar mazauna… bisa ga shaidar da aka bayar a lokacin".

A cikin sabbin bayanan kudaden da aka fitar, kamfanin da ke mallakar Prestwick Care, Malhotra Care Homes Limited, ya samu ribar £9.3m a cikin shekarar ta 2021-22. Wani akanta Vivek Kotecha ya ce hakan yana da girma sosai ga gidan kula da masu rauni. Yana tunanin cewa bayanin hakan na iya zama cewa kudaden da kamfinin ke kashewa kan ma'aikata bai ka na sauran kamfanoni ba.

"Wannan wani nau'in damuwa ne," in ji shi, "saboda irin waɗannan marasa lafiya suna buƙatar ma'aikata da kulawa ... in ba haka ba suna cikin hadarin fadowa ko kuma jin raunuka."

Corridor in Addison Court, with residents and worker
Bayanan hoto, Wani akanta ya ce da alama kudin da Prestwick Care ke kashewa akan ma'aikata bai kai na sauran kamfanoni ba

A watan Disambar 2022, mai'aikatar cikin gida ta Birtaniya ta dakatar da lasisin ɗaukar nauyin ma'aikatan kasashen ketare na Prestwick Care ba tare da ta bayar da wani dalilin daukar matakin ba.

Bayan haka, Bunty Malhotra ya kira ma’aikatan Addison Court 'yan kasar Indiya don halartar wani taro, inda ya yi kokarin shawo kan su ci gaba da zama.

Ya nuna cewa yana shirye ya yi watsi da duk wani kuskure da suka yi.

"Idan kuna aiki da NHS, kuskure ɗaya [sai a kai karar ku] gaban NMC (Majalisar jinya da ungozoma) kai-tsaye," in ji shi.

"Koyaushe za mu kare ma'aikatanmu, koyaushe za mu ce, 'wannan kuskuren batun horo ne'... ba a samun irin wannn kariyar waje."

Da ta ga bidiyon taron, Katy Maughan ta ce ta kadu kan yadda ya nuna a bayyane cewa yana kokarin tsoratar da ma'aikatan su zauna a gidan.

A cikin wata sanarwa da ta yi wa BBC, CQC ta ce tana sa ido sosai kan Addison Court tare da sauran wuraren da aka yi wa rajista a karkashin kamfanin. Ta kara da cewa idan akwai damuwar gaggawa game da lafiyar mutane, "za mu yi amfani da ikon da mu ke da ita wurin kiyaye mutane".

Prestwick Care ya ce duk wani zargin da aka yi na cewa ana aikata ba daidai ba rashin adalci ne kuma kuskure ne. Ya ce aminci da jin daɗin ma'aikatan ya kasance abu mafi mahimmanci a garesu, kuma "sun himmatu sosai don bincikar duk matsalolin da suka taso, da ɗaukar matakan da suka dace kamar yadda ya cancanta".