'Mun dauki kaddara game da masarautar mu da aka rushe'

Aliyu Ibrahim Abdulkadir

Asalin hoton, facebook Gaya

Bayanan hoto, Alhaji Aliyu Ibrahim Abdulkadir
An wallafa

Sarkin masarautar Gaya ta jihar Kano daya daga cikin masarautu biyar da gwamnatin jihar Kano ta rushe, ya ce sun karbi wannan al’amari hannu-bibiyu a matsayin wata kaddara daga Allah.

Alhaji Aliyu Ibrahim Abdulkadir ya shaida wa BBC cewa haka Allah ya nufa, don haka ba su jin haushin kowa:

''Ai kowa wannan abu ya same shi, ba zai ji dadi ba, to amma Allah ne ya kawo ka, komai akwai ajalinsa.

“Allah ya rubuta da ma tun kafin a haife mu hakan za ta kasance, saboda haka mu ba mu jin haushin komi.

“Wannan yin Allah ne mun karbe shi hannu-bibiyu,'' in ji shi.

Mai martaba Sarkin Gaya ya yi bayani kan halin da ake ciki bayan umurnin awa 48 da gwamnan jihar Kano ya bayar ga sarakunan da su fice daga masarautunsu.

A cewarsa ‘su ma su bin doka ne, kuma ba su ma bari awanni sun cika, suka bi doka suka fita’.

An dai samu wasu a masarautar Kano da suka garzaya kotu har ma suka samo oda ta kotu da ta dakatar da dokar soke masarautun, wadda gwamna Abba Kabir ya sanya wa hannu.

Sai dai sarkin na Gaya wanda aka sauke Alhaji Aliyu Ibrahim Abdulkadir ya ce sam ba su yi wannan tunani ba:

‘’Mu masu karbar kaddara ne, haka Allah ya so kuma haka za a yi dole, ba mu da niyyar mu je wajen shari’a, mun karbi kaddara, mun gode wa Allah’’.

Sarkin ya ce fatansa ga masarautar Gaya da alummar Kano shi ne Allah ya ba su zaman lafiya da arziki mai dorewa kuma ya zaunar da su lafiya.

Ya kuma yi kira ga alummar masarautar Gaya da su yi hakuri.

’Zan iya karbar sarki mai daraja ta biyu’

Bayan soke masarautun na Kano, bayanai sun nuna cewa gwamnatin jihar na duna yiwuwar majalisar dokokin jihar Kano za ta zauna ta yi nazari a kan duba yiwuwar samar da sarakuna masu daraja ta biyu.

Game da haka ne sarki ya ce zai yi maraba da hakan kuma zai karbi wani tayin sarki mai daraja ta biyu idan gwamnati ta yi masa hakan.

‘’Za mu karba a guje ma kuwa, tunda mun gaje ta’.

''Mu a wajenmu jama’a ce a gabanmu, duk abin da aka ce mu zo mu yi don jama’armu, mu taimaka musu, za mu yi shi saboda haka mu ba mu da haushin kowa mun karbi wannan kaddara, haka Allah ya so'' in ji shi.

A makon nan ne Majalisar dokokin jihar Kano ta yi gyara kan dokar masarautun jihar, abin da ya sa aka rushe masarautu biyar ciki har da masarautar ta Gaya.