Waiwaye: Karyewar farashin abinci da tankiyar Sanata Akpabio da Natasha

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 4

Farashin kayan abinci na sauka a Najeriya

Hatsi

Asalin hoton, Getty Images

Bayan ƴan Najeriya sun shafe shekaru suna kokawa kan tashin farashin kayan abinci da na masarufi, a yanzu bayanai na nuna yadda kayan abinci ke ci gaba da faɗuwa a kasuwanni.

Yanzu haka buhunan kayan amfanin gona, kamar masara da waken soya na ci gaba da faɗi, wani abu da ake ganin zai iya sassauta tsadar rayuwa da al'ummar ƙasar ke ciki.

Wasu matakan tattalin arziƙi da gwamnatin ƙasar ta fito da su - kamar cire tallafin man fetur da sauye-sauye a ɓangaren kuɗi - sun sanya kayan masarufi sun yi tashin gwauron zabi, lamarin da ya jefa al'umma cikin garari.

Tankiyar Sanata Akpabio da Natasha a majalisa

Sana Akpabio da Sanata Natasha

Asalin hoton, Nigerian Senate/X

Tankiya ta ɓarke a zauren majalisar dattawan Najeriya ranar Alhamis tsakanin shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio da sanata Natasha Uduaghan da ke wakiltar tsakiyar jihar Kogi.

Al'amarin dai ya janyo har shugaban majalisar, Akpabio ya umarci ɗaya daga cikin masu yi wa sandan majalisar hidima da ya fitar da sanata Natasha daga zauren majalisar.

Gidan talbijin na AIT ya rawaito cewa rikicin ya samo asali ne lokacin da mai tsawatarwa na majalisar, sanata Mohammed Munguno ya shaida wa ƴan majalisar cewa sanata Natasha ta ƙi amince wa ta koma sabuwar kujerar da aka ware mata.

Majalisa ta gayyaci shugabannin tsaro kan zargin USAID da bai wa Boko Haram kuɗi

Akpabio

Asalin hoton, Nigerian Senate

A tsakiyar makon nan ne Majalisar Dattawan Najeriya ta gayyaci shugabannin hukumomin bayanan sirri da na tsaron ƙasar su gudanar da bincike kan zargin hukumar raya ƙasashe ta Amurka, USAID da tallafa wa ta'adanci a ƙasar

A farkon makon ne ɗanmajalisar wakilan Amurka, Perry Scott ya zargi USAID da samar da kuɗaɗe ga ƙungiyoyin ta'addanci ciki har da Boko Haram.

Majalisar ta zartar da hakan ne bayan da Sanata Mohammed Ali Ndume, ya gabatar da buƙatar binciken.

Ndume ya buƙaci majalisar ta ɗauki maganar da muhimmanci bisa la'akari da iallar da 'yan ta'adda musamman ma Boko Haram suka yi.

Gwamnatin Najeriya za ta ɗauki ma'aikatan lafiya 28,000 saboda janye tallafin USAID

Ministan lafiya na Najeriya

Asalin hoton, Ali Pate

A farkon makon ne kuma ministan lafiya na Najeriya, Ali Pate ya ce gwamnatin ƙasar na duba yiwuwar ɗaukar mutum 28,000 - da a baya ke aiki da hukumar ba da agaji ta Amurka United States Agency for International Development (USAID).

Da yake magana yayin wata hira da gidan talabijin na Channels TV, ministan ya ce gwamnatin tarayya na da niyyar gyara ɓangaren kiwon lafiyar ƙasar yayin da Amurkar ke janye tallafin da take bayarwa ta hannun USAID.

Bayan hawansa mulki ne Shugaban Amurka Donald Truymp ya umarci a dakatar da bayar da tallafi wajen samar da magunguna da ayyuka kamar na cutar HIV a ƙasashe masu tasowa har sai an kammala bincike kan lamarin.

Gwamnan Katsina ya raba wa mata awaki

Gwamnan Katsina yayin rabon awaki

Asalin hoton, Katsina State Govt.

A cikin makon ne kuma gwamnatin jihar Katsina da ke arewa maso yammacin Najeriya ta bai wa mata 3,610 da ke gundumomi 361 tallafin awaki, a wani mataki ya yaƙi da talauci.

Gwamnan Jihar, Dikko Radda ya ce shirin wani babban mataki ne na cimma burinsa na ganin jihar Katsina ta zama kan gaba wajen yin kiwo a arewacin Najeriya da ma ƙasar baki ɗaya.

Dikko Rada ya kuma ce ƙarƙashin shirin za a horar da mata kan matakan kiwo da suka dace, kamar abincin da ya kamata su ci, kula da lafiyarsu, da ma dabarun noma.

IBB ya ƙaddamar da littafin tarihin rayuwarsa

IBB

Asalin hoton, Getty Images

A ranar Alhamis, 20 ga watan Fabrairu ne aka yi taron ƙaddamar da littafin tarinin tsohon shugaban ƙasar mulkin soja a Najeriya, Janar Ibrahim Badamasi Babangida.

Littafin mai suna " A Journey in Service" wanda tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Farfesa Yemi Osinbajo ya yi bitarsa, ya ce Cif Abiola na jam'iyyar SDP ne ya samu nasara kan Alhaji Bashir Othman Tofa na jam'iyyar NRC .

Abin da ya fi jan hankalin mutane shi ne yadda a karon farko, IBB ya fito ya bayyana cewa Cif Mashood Bashorun Abiola, ɗantakarar shugabancin Najeriya a ƙarƙashin jam'iyyar SDP a 1993 ne ya ci zaɓen da aka soke.

"Lallai Mashood Abiola shi ne ya lashe zaɓen shugaban ƙasa a 1993 bayan da ya samu ƙuri'u fiye da miliyan takwas inda ya samu nasara a kan Bashir Othman Tofa na jam'iyyar NRC mai ƙuri'a fiye da miliyan biyar." In ji Janar Babangida a cikin littafin da ya rubuta da kansa.

Kuɗaɗe da kadarorin da kotu ta ƙwace daga tsohon gwamnan CBN, Emefiele

Godwin Emefiele

Asalin hoton, Getty Images

A ranar Juma'a ce wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Legas a kudu maso yammacin Najeriya ta yanke hukuncinta na ƙarshe, inda ta ƙwace tare da miƙa wa hukumar yaƙi da rashawa ta Najeriya, EFCC, kuɗaɗe da kuma wasu kadarorin tsohon gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele.

Emefiele dai tsohon gwamnan bankin CBN ne da ya kwashe shekara tara yana jagorancin bankin, amma ya fara fama da ƙalubale tun daga watan Yunin shekarar 2023, bayan Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya sallame shi daga aiki.

A lokacin da take yanke hukunci, mai shari'a Yellim Bogoro ta amince da buƙatar da EFCC ta shigar ta hannun mai wakiltar ta, Bilkisu Buhari-Bala, bayan watsi da buƙatar da ɓangaren Emefiele ya shigar na dakatar da sauraron ƙarar.