Yadda aka koma gidan-jiya a Gaza

....

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Masu jimami sun taru ranar Litinin a kan gawarwakin yan uwansu, da hare haren Isra'ila suka kashe da tsakar dare a asibitin al-Aqsa, da ke Deir al-Balah
    • Marubuci, Frances Mao
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 6

Daren ya fara ne kamar kowane dare a Gaza, al'umma sun tashi da asuba suna yin sahur na azumin Ramadana. Bayan kwana 50 na tsagaita wuta, za a iya cewa ƙura ta lafa har mutane sun fara tunanin komawa harkokinsu.

To amma sai gari ya ɓarke da ƙarar bindiga da ta bama-bamai. Sai kuma kururuwa da ihun mutane ya biyo bayan hakan.

Essam Abu Oden da iyalinsa, na barci, lokacin da jiragen yakin suka kaddamar da hare harensu.

Wajen karfe 02:00 na tsakar dare, kwatsam karar bama bamai ta tashe su, kamar yadda ya shaida wa gidan rediyon BBC Gaza.

'Yata ce ta tashe ni, ta shaida mani abun da ke faruwa, nan da nan muka buya a bayan katanga, duk da muna tsoron gini zai iya fado mana''

Jiragen yakin Isra'ilar sun kutso ne daga Arewa, suka fara luguden wuta a tsakiyar Gaza, daga nan suka suka durfafi kudanci, yankunan Rafah da Khan Younis.

Hare haren na tsakar daren Litinin sun halaka sama da mutane 400, yawanci mata da kananan yara, kamar yadda ma'aikatar lafiya ta Hamas ta sanar, amma ita Isra'ila ta ce kai kai harin ne kan mayakan Hamas.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Sama da mutane 600 ne suka raunata.

An sake tsinitar kai a wani yanayi da asibitoci suka yi cikar kwari, yayin da likitoci da tsakar daren ke ta fadi tashin kula da mutane, yawanci mata da kananan yara.

BBC ta zanta da dangin wani da aka raunata, Ahmad Mo'in al-Jumla, a asibitin al-Shifa da ke birnin Gaza. lamarin ya rutsa dashi a matsugunin yan gudun hijira na al-Ahrar da ke gabar ruwa.

''Mun yi mamaki da aka kai hari wannan wuri, a cewar 'yar uwarsa, tana mai cewa dukkan yan uwansa sun kasa sanin inda yake a lokacin da lamarin ya faru''

''Daga tsakar dare har zuwa wayewar gari bamu iya gano inda yake ba, saboda yanayin tashin hankalin da aka tsinci kai a ciki a wajen, gaba daya ginin wajen ya rikito kan mutane''

Iyalinsa ma sun shiga wani yanayi lokacin da aka kai hari layinsu.

''Kwatsam, sai muka ga gini yana rikitowa kanmu, baraguzai na zubowa ta kowanne bangare, inji 'yar uwarsa''.

''Mun yi kokarin ficewa, don tsira da rayukanmu, amma babu komai a wajen, saboda cikin dare ne, kuma ana ta luguden wuta a ko ina

...

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Wani harin Isra'ila ya rusa wannan gidan a Deir al-Balah

''Hare haren sun dawo ne ba zato ba zato ba tsammani, babu wani gargadi, a cewar wani mazaunin Gaza''

Ya tashi yin sahun da asuba, lokacin da aka fara kai hari layinsu.

''Mun shiga yanayi na tashin hankali'' inji shi ''Kowa ya fada yanayin tsoro da rashin sanin inda zai dosa, idan lamarin ya kai ga raba mu da gidajenmu''

''An tsinci kai a wani yanayi da fargaba da tsoro suka sake dawo mana, musamman kasancewar wannan na faruwa ne yayin da muke cikin watan Ramadana''

Ofishin firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu, ya ce shine ya ba da umarnin kai hare haren, bayan da Hamas ta ki sakin karin fursunonin da take rike da su, ko ma amincewa da yarjejeniyar da Amurka ta gabatar ta tsawaita yarjejeniyar tsagauta bude wuta da ta kare tun cikin watan Janairu.

Tun lokacin da yarjejeniyar ta kare ne ake fargabar sake barkewar rikicin, musamman kasancewar tattaunawar zaman lafiyar ma ta tsaya cik.

Isra'ila ta sanar da fadar White House shirinta na dawowa ci gaba da kai hare hare kafin daukar matakin, amma kuma wadanda hare haren suka rutsa da su a Gaza basu san ga abun da zai faru ba.

Don haka dawowar hare haren, ya kawo karshen zaman lafiyar da aka shafe wata biyu ana yi, mai cike da rauni.

''Na kadu, da aka sake dawowar hare haren, amma abu ne dama da muka yi tsammani daga Isra'ila'' inji Hael,wani mazaunin Jabalia al-Balad, da ya yi magana da sashen larabci na BBC.

''Bamu yi mamaki ba, mun yi tsammanin hakan a kowanne lokaci, amma dai mun kadu sosai matuka, an kashe mutane kusan 200 a dan takaitaccen lokaci, a matsayi na na dan nan, na gaji da wannan abu, ya ishe mu haka, shekara daya da rabi kenan muna cikin wannan hali, ya isa haka'' inji shi.

Kafin yarjejeniyar a karshen watan Janairu, an shafe watanni 15 ana yakin, kuma haren haren Isra'ila sun halaka Falasdinawa dubu arba'in da shidda a wannan lokaci.

Umm Mohammed Abou Aisha, da ke zaune a Deir al-Balah a gabashin Gaza, ta iya yin rayuwa da mahaifiyarta tsawon wannan lokaci.

Sai dai an kashe mahaifiyarta a ranar Talata da safe. Abun da take iya tunawa da ita kawai shine ta zo shiga kicin, tana cewa za ta dafa abincin sahur.

''Mahaifiyata ta tashi da zummar dafa mana abincin sahur kamar yadda ta saba, don za mu tashi da azumi ba wai da yaki ba'' kamar yadda ta shaida wa kamfanin dillacin labarai na Reuters.

Umm Mohammed Abou

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, An kashe Umm Mohammed Abou, mahaifiyar Aisha da aka kashe a wani hari a gabashin Gaza

Harin ya rutsa da gidan makocinsu, inji ta.

Ta nuna damuwa kan yanayin da ake ciki, inda ta ce wani abu da ya yi aiki a yarjejeniyar da aka amince da ita.

Shima wani mazaunin wurin Muhammad Bdeir, ya ce an kashe 'yara a wannan waje, lokacin daka kai hari kan gidansu suna tsaka da barci.

''Kwatsam muka tashi muka ji ana luguden wuta, sun kai hari kan makwabtanmu, da muake je aikin ceto, sai muka ga wata yarinya a kasan baraguzai, muka ciro ta, da iyayenta, a nan ne nima ya ga 'yata.

...

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Wasu Falasdinawa da ke nuna damuwarsu kan hare haren Isra'ila da suka rutsa da gidajensu kenan a Jabalia.

A kudu maso gabashin Gaza, Ramez Alammarin, mai shekara 25, ya bayyana yadda ya rika daukar yara yana kaisu asibiti.

''Sun sake kaddamar da mummunan hari kan Gaza, kamar yadda ya shaida wa AFP, inda ya kara da cewa da idonsa, ya ga sassan jikin mutane warwatse a kan titi, su kuma wadanda suka raunata ba su iya samun kulawar likitoci ba.

Masu ruwa da tsaki kan asibitocin Gaza, sun shaida wa BBC cewa marasa lafiya da dama da aka kai masu, na fama ne da raukan da suka shafi kwakwalwa, da zubar jini da karaya da tsagewar kashi.

''Munin wannan al'amari ya sa an samu yawan marasa lafiyar da sun yi yawa ga likitocin da ake da su'' inji Dr Mohammed Zaqout, daraktan hukumar kula da asibitocin zirin Gaza.

Ya ce asibitoci guda bakwai ne kacal ke aiki a Gaza a wannan lokaci, bayan shafe watanni 15 ana wannan yaki. Kuma duk da yarjejeniyar tsagaita wutar da aka cimma kayan aikin lafiya kalilan aka iya shigar da su yankin.

Shima wani likita ya bayyana yanayin da ake ciki a matsayin mai muni, inda ya ce akwa karancin kayan aikin lafiya da magunguna.

''Hatta su kansu jami'an lafiya sun gaji, bayan shafe sama da shekara guda da rabi ana wannan yaki'' inji Dakta Muhammad Abu Salmiya''.

''Mun ga marasa lafiya da dama da suka rasu a gabanmu saboda kawai babu magunguna ko ma wata hanya da za a iya ba su kulawa''.

Ya bayyana matakin an Isra'ila a matsayin kisan kiyashi, kan yan Gaza yayin da suke tsaka da barci a gidansu.

Zuwa yanzu, yawancin wadanda aka kwantar na asibitin Nasser ne, da ke Khan Younis, a kudancin Gaza. an yi ta kawo marasa lafiya a kekunan tura masu nakasa.

Haka nan an yi ta kwasar gawarwakin mutane a fararen yaduka zuwa mutuwaren wannan sibiti. Mutane sun rika taruwa a kan titi don yi wa 'yan uwansu salla.

Essam, wanda 'yarsa ta tasa da safen nan, ya ce yana rokon kasashen da ke shiga tsakani su taimaka wajen kawo karsen wannan balai.

''Bama so a ce wannan yaki ya dawo, muna neman zaman lafiya, ta yadda za mu iya rayuwa, mu kuma yi barcinmu lami lafiya, ba tare da wata fargaba ba'' kamar yadda ya shaida wa BBC.