Me ke faruwa da babban hafsan sojin ƙasa na Najeriya Janar Lagbaja?

Asalin hoton, Nigerian Army
Har yanzu ƴan Najeriya na ci gaba da neman sanin haƙiƙanin abin da ke faruwa da babban hafsan sojin ƙasar, Laftanar Janar Taoreed Lagbaja, bayan jita-jitar mutuwarsa da wasu suka fara yaɗawa a ƙarshen mako.
Sai dai rundunar sojin ta Najeriya ta musanta rahotonnin mutuwarsa, inda ta ce hutu ya tafi ƙasar waje da kuma duba lafiyarsa.
Tun a makon jiya ne aka fara raɗe-raɗin cewa babban hafsan ya rasu a sanadiyar cutar kansa a wani asibiti a ƙasar waje, inda masu yaɗa maganganun suka riƙa cewa an ɓoye rasuwar ne saboda masu rububin neman maye gurbinsa.
Jaridar Sahara Reporters da ake bugawa ta intanet ta ruwaito cewa babban hafsan sojin yana fama da rashin lafiyar da ba ta ambata ba, inda ta yi iƙirarin cewa ciwon ya yi tsanani.
Wani mai suna Jackson Ude, wanda rubutunsa ya ja hankali sosai - har ta kai rundunar sojin ƙasan ta yanko saƙon da ya wallafa a shafinsa kuma ta musanta batun - ya ce babban hafsan sojin ya rasu sakamakon cutar kansa a wani asibiti a ƙasar waje.
Shi ma ya ƙara da cewa ana ɓoye-ɓoye ne saboda yadda wasu janar-janar da suke sha’awar maye gurbinsa suka fara rububi.
Me ke damun Janar Lagbaja kuma yana ina?
Da take bayani game da haƙiƙanin abin da ke faruwa, rundunar sojin ƙasa ta Najeriya ta siffanta labaran da ake yaɗawa da "ƙanzon-kurege" tana mai cewa shugaban sojin ƙasan yana raye kuma "babu wani giɓin shugabanci" a rundunar.
Cikin wata sanarwa, kakakin rundunar, Manjo Janar Onyema Nwachukwu, ya bayyana cewa shugaban nasu hutu ya tafi.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
"An yi duk wasu tsare-tsaren da suka dace domin shugaban tsare-tsare na rundunar wato chief of policy and plans, Manjo Janar Abdulsalami Ibrahim, ya ci gaba da jan ragamar rundunar kafin babban hafsan ya dawo," in ji sanarwar.
Sanarwar ta ƙara da cewa: "Wannan ba wai a rundunar sojin ƙasa kaɗai ya tsaya ba, akan samu yanayin da manyan hafsohin sukan yi tafiya har na tsawon wata uku, amma kuma a duk lokaci irin haka shugaban tsare-tsare ne yake cigaba da aikin babban hafsan.
"Don haka maganar cewa akwai giɓin shugabanci jita-jita ce kawai domin duk wasu harkokin sojin ƙasan babu wanda ya tsaya."
Sanarwar ta rundunar sojin ƙasa ta tabbatar da cewa janar ɗin ya je wata ƙasar waje domin duba lafiyarsa, sai dai ba ta bayyana ƙasar ba da kuma larurar da ke damunsa.
Wata sanarwar kuma da hedikwatar tsaron Najeriya ta fitar ranar Litinin ta ce lafiyarsa ƙalau, kuma ta ce babu maganar muƙaddashin shugaba a dokokin sojin Najeriya.
"Babban hafsan sojin ƙasa lafiyarsa ƙalau kuma nan gaba kaɗan zai ci gaba da aikinsa da zarar hutun ya ƙare," a cewar sanarwar da Birgediya Tukur Gusau ya fitar.
Lagbaja, wanda aka haifa a ranar 28 ga watan Fabrairun 1968 a jihar Osun, ya zama babban hafsan sojin ƙasa na Najeriya ne a watan Yunin 2023, inda ya zama babban hafsan sojin ƙasa na 27 bayan maye gurbin Faruk Yahaya.
Shin akwai babban hafsan riƙon ƙwarya a soji?
A cikin sanarwar rundunar sojin ƙasa, an yi amfani da kalmar "act" domin bayyana cewa Manjo Janar Abdulsalami Ibrahim ne zai ja ragamar rundunar a madadin Janar Lagbaja har zuwa lokacin da zai koma bakin aiki.
Wannan kalmar ce ta haifar da ruɗani, inda wasu suke cewa ba su taɓa jin an yi shugaban riƙon ƙwarya na soji ba.
Sai dai kuma a tata sanarwar, hedikwatar tsaron Najeriya ta ce babu wani muƙamin babban hafsan riƙon ƙwarya a rundunar, sannan ta ƙara da cewa Janar Taoreed Lagbaja ya tafi hutu ne na shekarar 2024.
"Shugaban tsare-tsare na rundunar sojin Najeriya Manjo Janar Abdulsalam Bagudu Ibrahim yana sanar da babban hafsan sojin ƙasan yadda al'amura suke tafiya," a cewar sanarwar.
Ta ƙara da cewa babu daɗewa Babban Hafsan Tsaron Ƙasa, Janar Christpher Musa, ya yi magana da Janar Lagbaja.
Daga ƙarshe rundunar ta jaddada gargaɗi ga masu neman sojoji su yi juyin mulki, tana mai cewa "hakan cin amanar ƙasa ne".









