Abu bakwai kan zaɓen ƙananan hukumomin jihar Kano na yau Asabar

Asalin hoton, Getty Images
A yau Asabar ne dai, jihar Kano ke bin sahun sauran jihohin ƙasar 36 wajen gudanar da zaɓen ƙananan hukumominta bayan kwashe kwanaki ana kai ruwa rana.
To sai dai ba kamar a wasu jihohi da dama zaɓen ƙananan hukumomin na Kano na cike da taƙaddama.
Ga wasu abubuwa da ya kamata ku sani dangane da zaɓen na ƙananan hukumomin jihar Kano:
1) Jam'iyyu guda shida ne za su fafata
Shugaban hukumar zaɓen jihar Kano ta Kansiec, Farfesa Sani Lawan Malumfashi ya ce babu gudu babu ja da baya hukumarsa za ta gudanar da zaɓukan a ƙananan hukumomi na jihar Kano ranar Asabar domin sun shirya tsaf.
Sai dai farfesa ya ce abin takaici daga cikin jam'iyyu 19 guda shida kacal suka shiga zaɓen kamar haka;
- AA
- ZLP
- ACCORD
- AAC
- NRM
- NNPP
Wannan dai na nuni da cewa manyan jam'iyyun adawa na jihar ta Kano wato APC da PDP duka ba su shiga zaɓen ba.
2) Za a yi zaɓe a ƙananan hukumomi 44
Jihar Kano kasancewarta mafi yawan al'umma a Najeriya bisa alƙaluman ƙidayar 2006, ta na da yawan ƙananan hukumomi guda 44 fiye da kowace jiha a ƙasar.
Farfesa Sani Lawan Malumfashi ya ce hukumarsa ta KANSIEC ta shirya tsaf domin gudanar da zaɓen a dukkannin ƙananan hukumomin 44.
3) Hukuncin kotuna uku kan zaɓen
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Hukuncin babbar kotun jiha: A ranar Juma'a ne wata babbar kotun jihar Kano ta umarci hukumar zaɓe ta jihar ta ci gaba da shirin gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi da ta shirya yi ranar Asabar, bayan wata kotun tarayya ta hana yin hakan.
Hukuncin babbar kotun tarayya na 1: Hukuncin kotun ta jiha na zuwa ne bayan na babbar kotun tarayya ƙarƙashin Mai Shari'a Simon Amobeda, ya dakata da zaɓen bayan rushe hukumar zaɓen ta Kano wato Kano State Independent Electoral Commision (Kansiec) bisa gamsuwa da ya yi cewa shugabanninta ƴan jam’iyyar NNPP ne mai mulkin jihar.
Lauyan da yake wakiltar hukumar zaɓe, Muntari Garba Ɗandago, ya faɗa wa manema labarai cewa kotun ƙarƙashin Mai Shari'a Sanusi Ma'aji ta ce babu hujjar da ke tabbatar da cewa shugabannin Kansiec 'yansiyasa ne. A saboda haka a ci gaba da zaɓe.
Hukuncin babbar kotun tarayya na biyu: A wani hukuncin kuma na daban babbar kotun tarayyar da ke Abuja ƙarƙashin mai shari'a Simon Amobeda ta sake bayar da wani sabon hukunci ranar Juma'a inda ta yanke hukunci guda uku kamar haka:
- Kotu ta hana hukumar zaɓe ta Najeriya, INEC ta bai wa hukumar zaɓen jihar Kano jerin sunayen masu zaɓe.
- Ta umarci hukumar zaɓen jiha wato Kansiec da ta karɓi jerin sunayen ƴantakarar ɓangaren Dalhatu Shehu wanda a cewar kotun shi ne doka ta sani a matsayin shugaban jam'iyyar NNPP na Kano kuma daga shi ka da ta karɓi na kowa.
- Kotu ta hana jami'an tsaro samar da tsaro a ranar zaɓen.
4) Abin da jami'an tsaro suka ce kan zaɓen

Asalin hoton, KIYAWA/FACEBOOK
Bayan hukuncin babbar kotun ta tarayya da ta dakatar da zaɓen da rushe hukumar zaɓen, sai kakakin rundunar ƴansandan Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya fitar da sanarwar cewa sun samu hukuncin kotu da ta buƙaci su koma gefe a ranar zaɓen.
Sai dai kuma rundunar ƴansandan ta ce jami'anta za su fito su yi sintiri domin samar da tsaro ba tare da sun shiga harkar zaɓen ba.
To amma bayan sabon hukunci daga babbar kotun jiha na ci gaba da gudanar da zaɓen kamar yadda aka tsara, sai mai magana da yawun rundunar ƴansanda, SP Abdullahi Kiyawa ya ce kwamishinan ƴansanda jiahr Kano, CP Salman Garba Dogo ya umarci jami'ansu da su fito domin kare dukiya da rayukan al'ummar jihar.
Kafin nan dai rahotanni sun ta ambato cewa hukumar zaɓen ta ce za ta yi amfani da jami'an Hisbah a rumfunan zaɓe domin tabbatar da zaman lafiya.
5) APC ta gargaɗi gwamnatin Kano kan zaɓen

Asalin hoton, Alfindiƙi/Facebook
Shugaban jam'iyyar APC mai adawa a jihar Kano, Alhaji Abdullahi Abbas ya gargaɗi gwamna Abba Kabir Yusuf da ka da ya kuskura ya gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi "kamar yadda wata kotu bayar da umarni."
A wata sanarwa da jam'iyyar ta fitar ranar Juma'a a Abuja, Abdullahi Abbas ya ce ya kamata gwamna Abba Kabir Yusuf ya sani cewar idan har ya ci gaba da gudanar da zaɓen na to "tamkar ya gayyato rashin zaman lafiya ne a jihar ta Kano."
"Kawai gwamna ya bi umarnin kotu. A matsayinmu na masu son bin doka da oda da kuma son cigaban jiharmu ta Kano, dole ne gwamna ya guji duk abin da ka iya jefa jihar tamu cikin ruɗani." In ji Abdullahi Abbas.
6) Oktoba ne wa'adin da kotun ƙolin ta bayar na zaɓe
A watan Okotoba ne wa'adi na ƙarshe da kotun ƙoli ta bai wa jihohin ƙasar da su yi zaɓen na ƙananan hukumomi ko kuma su fuskanci fushin kotu da na gwamnati na hana su kuɗin wata-wata da gwamnatin tarayya ke ba su.
A watan Yulin ne dai kotun ta ƙoli ta yanke hukunci cewa dole ne jihohin ƙasar su rinƙa bai wa ƙananan hukumominsu kuɗinsu na ɗauni na wata-wata, inda kuma jihohin suka nemi a ba su har zuwa watan Oktoban.
7) Zaɓen Kano na kama da na jihar Rivers

Masu lura da al'amura sun ce zaɓen jihar Kano da ke cike da taƙaddama ba shi da maraba da na jihar Rivers wanda shi ma aka yi ta turka-turka, inda har ta kai ga ƴan takarar ƴan jam'iyya mai mulki ta PDP ɓangaren gwamna mai ci, Siminalyi Fubara suka fice suka koma jam'iyyar APP wadda ta lashe ƙananan hukumomi 22 daga cikin 23.
A lokacin zaɓen dai na jihar ta Rivers, ƴan sanda sun ƙaurace wa akwtunan zaɓe bi sa umarnin kotu, wani abu da ya tilasta wa jihar amfani da al'ummar gari da ƴan sintiri domin samar da tsaro.
Rikice ne tsakanin tsohon gwamnan jihar ta Rivers kuma ministan birnin Abuja, Nyesom Wike da gwamna mai ci, Siminalayi Fubara irin ta tsakanin tsohon uban gida da yaronsa wadda ake gani irinta ce tsakanin Rabi'u Musa Kwankwaso da shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje.










