Faransa ta ajiye Mbappe a wasannin National League

A

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Kocin Fraansa Didier Deschamps ya ce matakin barin kyaftin ɗin Faransa Kylian Mbappe na rashin buga wasannin National Lig biyu na wannan watan iya wannan karon ne.

Ba a zaɓi dan wasan bayan Real Madrid ɗin ba cikin tawagar Faransa a wasannin da za ta fafata da Isra'ila da Italiya.

Ko a watan Oktoba sai da aka cire sunan Mbappe mai shekara 25 daga tawagar ƙasar da ta buga National Lig, wani uzuri da aka yi masa domin warkewa daga jinyar da ya yi wanda aka yi tsammanin zai buga wasan da za a yi a wannan watan.

"Na tattauna da shi, hukunci ne da na ɗauka kan waɗannan wasannin kawai," in ji koci. "Kylian ya so ya zo."

Dan wasan gaban da ya koma Real Madrid bayan ƙarewar kwantaraginsa a PSG, kuma ya gaza ƙoƙari irin wanda ya dace tun zuwansa Bernabue.

Mbappe ya ci kwallo takwas cikin wasanni 15 da ya buga a ƙungiyar ta La Liga inda ya ci kwallo ɗaya a wasansa biyar na farko.

Real da ta lashe Champons da La Liga a bara, ta sha kashi a hannun abikiyar hamayyarta Barcelona 4-0.

Mbappe wanda ya ci Kofin Duniya a 2018, ya ci kwallo 48 a wasa 86 da ya buga wa Faransa.