An bai wa Ingila gurbi biyar kai tsaye a Champions League a badi

Asalin hoton, Getty Images
Ingila ta samu gurbin Champions League biyar kai tsaye a baɗi, sakamakon da Arsenal ta doke Real Madrid 3-0 ranar Talata a Emirates.
Real Madrid ta sha kashi 3-0 a Emirates a wasan farko zagayen kwata fainal a Champions League.
Sai a ranar Laraba 16 ga watan Afirilu, Real Madrid za ta karɓi bakuncin wasa na biyu a Santiago Bernabeu.
Yanzu haka ƙungiyoyin da ke buga Premier League a gasar zakarun Turai a bana na bukatar cin wasa ɗaya nan gaba, domin a tabbatar mata da gurbin.
Kenan ana bukatr cin wasa ɗaya daga Arsenal ko Aston Villa ko Manchester United ko Tottenham ko kuma Chelsea a wasan gaba na zakarun Turai da suke buga wa.
Ana ware karin gurbi biyu a duk kaka ga kasar da ƙungiyoyinta suka haɗa maki da yawa, sakamakon yawan cin wasanni a ma'aunin Uefa coefficient table.
Ana sa ran Liverpool za ta lashe Premier League na bana, sai Arsenal ta biyu da Nottingham Forest biye da ita da Chelsea.
Sauran sun haɗa da Newcastle da Manchester City da Aston Villa da Brighton da kuma Bournemouth, wadda take ta 10, kuma maki 12 ne tsakaninsu.
Wata kila Ingila ta samu ƙungiya bakwai a Champions League a kakar 2025/26, idan Aston Villa ta lashe kofin zakarun Turai na bana, amma ta kasa samun gurbin a teburin Premier.
Haka kuma Ingila za ta samu karin ƙungiya da zarar Manchester United ko Tottenham ta lashe Europa League na kakar nan.
Italiya ce ta biyu da ake sa ran za ta samu gurbi biyar a shekara mai zuwa a Champions League, sai Sifaniya ta biyu da Jamus ta uku.











