Abin da ƴan Najeriya ke faɗa game da sabon kocin Super Eagles Labbadia

Asalin hoton, The Nigeria Football Federation/ Facebook
A ranar Talata ce Hukumar Ƙwallon Kafa ta Najeriya, NFF ta sanar da naɗa Bruno Labbadia a matsayin sabon kocin tawagar Super Eagles.
Labbadia ne zai maye gurbin Finidi Geroge, wanda ya ajiye aiƙinsa a watan Yuni, kwana kaɗan bayan ya zama kocin a matsayin kocin Najeriya 37.
Sabon kocin, wanda ɗan asalin ƙasar Jamus ne, tsohon ɗan wasan ƙasar Jamus ne, sannan ya buga ƙwallo a ƙungiyoyi da dama ciki har da Hamburger SV da Bayern Munich da FC Cologne da Werder Bremen da sauransu, inda har ya taɓa lasje lashe kofin Bundesliga a ƙungiyar Bayern Munich a 1994.
Ya horar da ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa irin su Hertha Berlin da VfB Stuttgart da VfL Wolfsburg da Hamburger SV da kuma Bayer Leverkusen da sauransu.
Kafin a naɗa shi kocin tawagar, an yi ta raɗe-raɗin cewa za a naɗa Herve Renard, wanda ya kafa tarihin lashe Gasar Cin Kofin Nahiyar Afirka sau biyu a kasashe biyu daba-daban; Ƙasar Zambia a 2012 da Ivory Coast a 2013, sannan ya lashe Kocin Nahiyar Afirka a shekarun 2012 da 2015 da 2018.
Abin da ake faɗa a game sabon kocin
Duk da cewa sabon kocin ya horar da ƙungiyoyi da dama, wasu ƴan Najeriya suna ganin kamar kocin bai cancanci jan ragamar tawagar ba, wadda ita ce giwar Afirka.
Wani mai suna Daniel C. Ikwuaguw ya rubuta a ƙarƙashin sanarwar naɗa sabon kocin cewa a takarda, ko Emmanuel Amuneke ya fi sabon kocin.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 1
Shi ma wani sunan It's Me a shafin X, ya rubuta a ƙarƙashin sanarwar ta NFF cewa, "ku ne matsalar ƙwallon Najeriya, kuna ɗaukar masu horarwa waɗanda ba su cancanta ba, waɗanda suke amfani da Super Eagles su samu ɗaukaka a duniya. Sai ku riƙa ɗauko mana masu horarwa da sai mun shiga google muke iya gane su wane ne."
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 2
Shi ma wani mai suna Oni Seun Paul ya ce, "bayan damunmu da surutu da kuka yi, wannan kocin wanda bai da wani tarihi mai kyau kuka ɗauko mana. Finidi ma sai ya fi wannan amfani."
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 3
Wani mai amfani da sunan MY Authentic ya rubuta cewa, "wannan da kuke sanar da sabon koci da tsakar, ina fata dai ba cinikin bayan fage ne" mu dai kawai mu ga sakamako mai kyau."
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 4
Shi ma Ilyas ya ce, "wai ina kuke samu irin waɗannan mutanen ne?"
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 5