Daga Usman Minjibir, Aisha Babangida da Isiyaku Muhammed
Mawaƙa sun hana Donald Trump amfani da kaɗe-kaɗensu a yaƙin neman zaɓensa
Asalin hoton, Reuters
Bayanan hoto, Mawaƙan sun haɗa da Beyoncé da Abba da Rolling Stones da Rihanna da Adele
Ƙungiyar mawaƙa ta, Abba, da ke Sweden ta zama ta baya-bayan nan da ta ƙi yarda Donald Trump ya yi amfani da waƙoƙinta wajen yakin neman zaɓensa.
Mawaƙan sun yi ƙorafi da cewa an yi amfani da waƙoƙi da bidiyonsu - da suka haɗa da waƙar ,''The Winner Takes it All,'' da kuma ''Money, Money, Money''- a wajen yakin neman zaben Trump ɗin a Minnesota a watan Yuli.
Sauran wasu mawaƙan da suka ƙi yarda tawagar yaƙin neman zaɓen ɗan takarar shugaban Amurkar na jam'iyyar Republican ta yi amfani da waƙoƙinsu su ne Rolling Stones da Rihanna da kuma Adele.
A kwanan nan kamfanin waƙoƙin Beyoncé ya fitar da wata anarwa ta gargaɗi bayan da aka yi amfani da waƙarta ta Freedom a wani bidiyo na yaƙin neman zaɓen Mista Trump.
Sai dai kamfanin ya ba wa abokiyar hamayyar Trump, wato Kamala Harris ta jam'iyyar Democrat damar yin amfani da waƙoƙin.
Tawagar Donald Trump ta yi sa-in-sa da mai kula da maƙabarta
Asalin hoton, Getty Images
Rundunar Sojin Amurka ta soki rashin natsuwar da ‘yan tawagar yaƙin neman zaɓen Donald Trump suka nuna yayin da suka kai ziyara a maƙabartar sojoji ta Arlington a ranar Litinin.
A cikin wata sanarwa da ta fitar, ta ce ɗaya daga cikin ma'aikatan Mista Trump ya yi gaggawar bankaɗe wani jami'in maƙabartar da ke ƙoƙarin aiwatar da dokar da ta haramta yaƙin neman zaɓe a harabar maƙabartar.
Rundunar ta ce jami'in maƙabartar ya nuna ƙwarewa a aikinsa, inda ta bayyana lamarin a matsayin abin takaici.
Ofishin yaƙin neman zaɓen Mista Trump ya musanta zargin, yana mai cewa jami'in na fama ne da matsalar taɓin hankali.
Ana ɗaukar maƙabartar Arlington da ke jihar Virginia da matuƙar muhimmanci inda a nan ne ake binne dakarun sojin Amurka da suka mutu a bakin daga.
WHO ta ce Isra'ila da Hamas sun amince a yi riga-kafin Polio a Gaza
Asalin hoton, Getty Images
Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO, ta ce rundunar sojin Isra'ila da ƙungiyar Hamas sun amince da tsagaita wuta na kwana uku-uku na wani tsawon lokaci domin a sami damar yi wa sama da yara dubu dari shida da ke Gaza allurar rigakafin cutar shan inna.
Da yake jawabi ga manema labarai ta hanyar bidiyo, wakilin hukumar ta WHO, a Gaza, Rik Peeperkorn, ya bayyana yadda aka cimma yarjejeniyar inda ya ce, : "An shirya aikin rigakafin ne tare da haɗin kan ma'aikatar lafiya da sauran abokan haɗin gwiwa.
Don haka, duk wasu masu ruwa da tsaki a Gaza sun amince da hakan sun kuma gudanar da wannan tattaunawar da hukumomin Isra'ila.
Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu ya jaddada cewa wannan tsarin ba wai yana nufin an tsagaita wuta dindindin ba ne a Gaza.
Ana gwabza ƙazamin faɗa tsakanin Ukraine da Rasha
Asalin hoton, Reuters
Shugaban sojojin Ukraine ya bayyana cewa ana gwabza ƙazamin fada da dakarun Rasha a gabashin ƙasar bayan shafe kwanaki da dama a fagen daga.
Janar Oleksandr Syrsky ya ce Rasha na kara ƙaimi a hare-haren da take kaiwa duk da nufin ƙwace iko da birnin Pokrovsk.
Wakilin BBC ya ce an ci gaba da kwashe mutane daga yankin amma an ce wasu mazauna garin na ci gaba da tattara abubuwan da suke buƙata a yayin da dakarun Rashan ke shirin yi wa yankin ƙawanya.
Tun da farko dai Moscow ta ce ta sake ƙwace wasu ƙauyuka biyu a yankin gabashi - ɗaya a kusa da garin Pokrovsk ɗaya kuma a yankin Luhansk.
Ukraine ta ce ɗaya daga cikin jiragen da NATO ta ba ta ya yi haɗari
Asalin hoton, Getty Images
Rundunar sojin Ukraine ta ce ɗaya daga cikin jiragen yaƙinta ƙirar F-16 wanda ƙawayenta na NATO suka ba ta ya yi hatsari a ranar Litinin kuma matuƙinsa ya mutu.
An yi amfani da jirgin ne a yunƙurin daƙile harin makami mai linzami na Rasha.
Sojojin sun ce matuƙin jirgin da ya mutu ya yi nasarar kakkaɓo makamai masu linzami guda uku da wani jirgin sama maras matuƙi kafin jirginsa ya sami tangarɗa.
Ana dai ci gaba da gudanar da bincike kan musabbabin faruwar lamarin.
Shugaba Bola Tinubu ya tafi China
Asalin hoton, @NGRPresident
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bar Abuja domin zuwa babban birnin China, Beijing a yau Alhamis 29 ga watan Agusta, don wata ziyarar aiki.
Shugaban na Najeriya zai yada zango na ɗan lokaci a Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa.
A China, shugaban zai gana da takwaransa Shugaba Xi Jinping sannan kuma zai gana da shugabannin 'yan kasuwa na China a gefen taron haɗin kai na tsakanin ƙasashen Afirka da China.
Manyan jami'an gwamnatin Najeriya na daga cikin waɗanda suka raka shugaban ƙasar, kamar yadda sanarwar da matimakinsa na musamman kan harkokin yaɗa labarai Chief Ajuri Ngelale ta ce.
Gwamnatin Najeriya ta ce ba za ta biya likitocin da ke yajin aiki albashi ba
Asalin hoton, STATE HOUSE
Bayanan hoto, Shugaban Najeriya Bola Tinubu
Gwamnatin Najeriya ta ce ba za ta biya likitocin da suka shiga yajin aiki na gargaɗi na kwana bakwai ba a asibitocin hukuma, tsawon kwanakin da suka ƙaurace wa aikin.
Likitocin sun shiga yajin aikin na barazana ne, inda suke buƙatar a sako abokiyar aikinsu, Dr Ganiyat Popoola, wadda masu satar jama'a suka sace wata takwas da ya wuce.
A wata sanarwa da ma'aikatar lafiya ta fitar yau Alhamis, ta nuna matuƙar damuwa a kan matakin likitocin masu neman ƙwarewa (NARD), na shiga yajin aikin, duk da abin da ta ce ƙoƙarin gwamnati na ganin an sako likitr lami lafiya.
Sanarwar ta ƙara da cewa akwai tattaunawa da yunƙuri na manya da ake shirin yi kan lamarin kuma hukumomi sun ce suna da ƙwarin gwiwa za a samu nasara.
Tun a watan Disamba na 2023 aka ace Dr Popoola mai 'ya'ya biyar tare da mijinta da kuma wani danginsu.
To amma an saki mijin nata a watan Maris bayan da aka ce an biya kuɗin fansa.
Ɓarayin na neman a biya su naira miliyan 40 ne kafin su sake su.
Hukumar Nukiliya ta Duniya ta ce Iran ta ci gaba da inganta makamashin yureniyon
Asalin hoton, OTHERS
Hukumar sa ido kan makamashin nukiliya ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce Iran ta ci gaba da sarrafa yureniyom (uranium) da za ta iya amfani da shi wurin ƙera makamai kuma ta ƙi ta ci gaba da bai wa jami'an hukumar haɗin kai.
Wani rahoto da hukumar ta IAEA ta fitar ya ce idan har ta ci gaba a haka Tehran za ta inganta yureniyom din da za ta iya ƙera makaman nukiliya guda huɗu.
Wakilin BBC ya ce Rahoton hukumar ya yi ƙiyasin cewa Iran wadda ta musanta cewa tana ƙera makaman nukiliya a halin yanzu tana da sama da kilogiram 160 na yureniyom wanda ta inganta har zuwa kashi sittin cikin ɗari
An fara shigar da kayan agaji Sudan - Jakadan Amurka
Asalin hoton, REUTERS/Zohra Bensemra
Jakadan Amurka na musamman a Sudan, Tom Perriello, ya ce an shigar da kayan agaji na kusan fan miliyan 6 zuwa ga yankunan da ake ɓukata a ƙsar t hanyoyi biyu da aka buɗe kwanan nan.
Dukkanin ɓangarori biyun da ke yaƙin basasar da a yanzu ya kai wata 16, suna hana shigar da kayan agajin, amma a farkon watan nan suka yi alƙawarin bari a shigar.
Perriello, ya gaya wa manema labarai cewa matsaloli na mutane da kuma waɗanda ba na mutane ba na haifar da matsala wajen kai kayan, inda ya bayar da misalin ambaliyar da aka yi kwanan nan bayan da madatsar ruwa ta fashe, kuma ya ce ana ƙoƙarin ganin an buɗe wata ƙofar ta uku.
Jakadan ya ce har yanzu akwai rashin kishi daga ɓangarorin masu yaƙin na gnin an kawo ƙarshen rikicin.
Ya yi kira na musamman ga dakarun RSF, da su daina ruwan bam da suke yi a kan jama'a barkatai, kamar yadda suke yi a makonnin nan.
Ƙungiyar ta tura wakilanta wajen tattaunawar zaman lafiya a Switzerland a tsakiyar watan Agusta, amma ita rundunar sojin Sudan ta ƙaurace wa zaman.
To amma Mr Perriello ya ce mambobin taron na tattaunawa a kai-a kai da dukkanin ɓangarorin biyu.
EU na shirin sanya wa Isra'ila takunkumi kan yaɗa kalaman ƙiyayya ga Falasɗinawa
Asalin hoton, AFP
Babban jami'in diflomasiyya na ƙungiyar tarayyar Turai Josep Borrell ya zargi wasu ministocin gwamnatin Isra'ila da furta kalaman nuna ƙyama ga Falasdinawa da kuma gabatar da ra'ayoyin da suka saba wa dokokin ƙasa da ƙasa.
Da yake magana kwana ɗaya bayan da Isra'ila ta ƙaddamar da wani gagarumin farmakin soji a Gabar Yamma da Kogin Jordan da ta mamaye, ya ce yana tuntuɓar mambobin ƙungiyar ta EU kan ko za su ƙaƙaba wa waɗannan ministocin takunkumi.
Tun da farko Sakatare Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya Antonio Guterres ya yi kira ga Isra'ila da ta gaggauta dakatar da ayyukan da take gudanarwa a Gaɓar Yamma, inda ya ce rashin yin hakan na ƙara taɓarɓara al'amuran tsaro a yankin.
Najeriya ta rage wa asibitocin gwamnati kashi 50 cikin ɗari na kuɗin wuta
Asalin hoton, Getty Images
Ƙaramin ministan Lafiya a Najeriya, Dakta Tunji Alausa ya sanar da cewa Gwamnatin Tarayya ta amince da bayar da tallafin kashi 50 cikin ɗari na kuɗin wutar lantarki ga asibitocin gwamnati a faɗin ƙasar.
A cewarsa, an yi hakan ne domin rage kuɗaden da ake kashewa wajen gudanar da asibitoci, da kuma rage wahalar da masu jinya suke sha.
Ministan ya bayyana haka ne a lokacin da ya kai ziyara asibitin Ƙwaƙwalwa da ke Barnawa a Kaduna domin ƙaddamar da fasahar adana bayanai da injin samar da lantarki (jannareto) a ɗakin aikin gaggawa na asibitin.
Haka kuma an mayar da ɗakin wankin ƙoda mai amfani da hasken rana.
Uefa ta karrama Ronaldo a matsayin wanda ya fi cin ƙwallo a tarihin Champions League
Asalin hoton, Getty Images
Cristiano Ronaldo ya samu lambar yabo ta kasancewa gwarzon ɗan wasan da ya fi zura ƙwallo a tarihin gasar Zakarun Turai ta Champions League.
Shugaban hukumar ƙwallon ƙafar Turai, Uefa, Aleksander Ceferin wanda ya miƙa wa Ronaldo kyautar a lokacin bikin fitar da jadawalin ''gasar da ta fi muhimmanci,'' in ji shi - Champions League, yau a birnin Monaco, na Faransa.
Ceferin ya ce an karrama Ronaldo da kyautar ne saboda babban tarihin da ya kafa a gasar ta Zakarun Turai.
Cristiano Ronaldo ya ce sabuwar kyautar da aka ba shi za ta samu muhimmin waje a dakinsa na adana kayan tarihi a Madeira.
Ɗan wasan na gasar Saudiyya ya ci jimillar ƙwallo 140 a kulob uku da ya buga wa wasa a Turai - su ne Manchester, da Real Madrid, da kum Juventus.
Ɗan ƙwallon na ƙasar Portugal mai shekara 39 ya shafe mafi tsawon rayuwar ƙwallonsa a ƙungiyoyin Sporting CP, da Manchester United, da Real Madrid, da Juventus, kafin ya koma Al-Nassr ta Saudiyya.
Shugaban na Uefa, ya kuma ce Gianluigi Buffon, wanda yana daga cikin masu fitar da jadawalin na yau, ya ce shi ne gwarzon mai tsaron raga a duk duniya.
Jami'an tsaro sun yi wa Bazoum tambayoyi
Asalin hoton, AFP
Bayanan hoto, Mohammed Bazoum
Jami'an sojojin da ke mulkin Nijar, sun yi wa hamɓararren shugaban ƙasar Mohamed Bazoum, tambayoyi kafin gurfanar da shi a gaban kotu bisa zargin laifin cin amanar ƙasa, kamar yadda shafin intanet na kafar yaɗa labaran Faransa, RFI, ya ruwaito a yau Alhamis, 29 ga watan Agusta.
Jandarmomi uku da wani kwamanda da kyaftin da kuma saja-manjo ne suka yi wa Bazoum tambayoyi tsawon shekara biyar a fadar shugaban ƙasar da ke Yamai, inda yake tsare tun bayan da aka hamɓarar da shi a watan Yuli na 2023.
Wasu kafofi da kafar ta RFI ta nuna sun ce, Bazoum y kare kansa sosai a kan dukkanin tambayoyin da suka yi masa.
Gwamnatin Nijar ƙarƙashin Birgediya Janar Abdourahmane Tiani ta zargi tsohon tsohon da babban laifin cin amanar ƙasa.
A ranar 14 ga watan Yuni ne, wata kotu ta tuɓe masa rigar kariyar da yake da ita, abin da ya bayar da damar gurfanar da shi a gaban kotu.
A watan Disamba na 2023, koun Ecowas ta zartar da cewa tsare shi da iyalinsa bai dace ba.
Sojojin Najeriya sun ce sun kashe ƴanbindiga sama da 1,000 a Agusta
Asalin hoton, Getty Images
Rundunar Tsaron Najeriya ta ce sojojinta sun kashe ƴan bindiga sama da 1,000 a cikin wannan watan a faɗin Najeriya.
Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Daraktan Rundunar Tsaron Najeriya, Manjo Janar Edward Buba, inda a ciki ya bayyana cewa aikace-aikacen sojin yana matuƙar daƙile ayyukan ƙungiyoyin ƴan bindigar.
"Muna sane cewa muna yaƙi ne da maƙiya marasa imani, wanda hakan ya sa dole mu ƙara ƙaimi wajen dakatar da su."
Ya ce daga shirye-shiryen sojojin, akwai takura ƴan bindigar domin hana su sakat, "sannan sojojin suna bibiyar kwamandojin ƴan ta'addan da yaransu da ma masu taimaka musu."
Ya ƙara da cewa tuni sun ga bayan wasu manyan kwamandojin ƙungiyoyin a watan "A Arewa ta Gabas an kashe irin Munir Arika da Sani Dilla (Aka Dan Hausawan Jibilarram) da Ameer Modu da Dan Fulani da Fari Fari da Bakoura Araina Chikin da Dungusu da Abu Darda da Abu Rijab."
Sanarwar ta kuma ƙara da cewa a yankin Arewa maso Yamma sojojin sun ga bayan manyan ƴan bindiga kamar su Kachalla Ɗan Ali
Garin Fadama da Kachalla Ɗan Mani Na Inna da Kachalla Basiru Zakariyya da Sani Baka
Tsine da Inusa Zangon Kuzi da Ibrahim da Tukur da Kamilu Buzaru da sauransu.
"Sojoji sun samu gagarumar nasara a kan ƴan bindigar, sannan kuma suna ci gaba da ƙara ƙaimi a aikace-aikacen da suke yi a yankunan Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya da Kudu maso Kudu da Kudu maso Gabas domin magance matsalar tsaron da ake fama da su."
Ya ce jimilla a watan Agusta, sojoji sun kashe ƴan ta'adda 1166, an kama guda 1,096 sannan an tseratar da waɗanda aka kama guda 721.
Haka kuma a cewar sanarwar, ak ƙwato makamai 391, da alburusai 15,234, sannan sun daƙile satar mai da aka ƙiyasta ya kai na Naira biliyan 5.
"Aikace-aikacen sojojin sun sa ƴan bindigar sun ja baya sosai, wanda hakan ya sa suke ta miƙa wuya, musamman a Arewa maso Gabas," in ji shi, sannan ya ƙara da cewa sojojin za su ƙara matsa lamba a sauran yankunan domin samun irin wannan nasarar."
HRW ta zargi dakarun RSF da na gwamnati a Sudan da aikata laifukan yaƙi
Asalin hoton, Getty Images
Kungiyar kare hakkin Dan'Adam ta Human Rights Watch, HRW ta zargi ɓangarorin da ke yaƙi a Sudan da aikata laifukan da suka haɗa da kisan gilla da kuma azabtar da mutanen da suke tsare da su.
Ƙungiyar ta yi nazarin bidiyo da dama da aka naɗa cikin shekara guda da ta gabata wanda ke nuna munanan ayyukan da dakarun sojin Sudan da na rundunar RSF da ƙawayensu ke aikatawa.
Kungiyar ta Human Rights Watch ta ce ganin yadda mayaƙan ke ɗaukar kansu hotuna yayin da suke aikata waɗannan laifukan na cin zarafi na nuni da yadda suka yi imanin cewa ba za a hukunta su ba .
Ƙungiyar dai ta ce ana buƙatar gudanar da cikakken bincike domin hukunta waɗanda ke da hannu a aikata waɗannan munanan laifukan.
Ambaliyar ruwa ta kashe mutum 179 a Najeriya
Asalin hoton, Getty Images
Ambaliyar ruwa ta kashe aƙalla mutum 179 a Najeriya sannan ta raba fiye da dubu 200 barin muhallinsu sakamakon kwashe makonni da aka yi a zabga ruwa kamar da bakin ƙwarya.
Hukumar bada agajin gaggawa ta Najeriya, NEMA ce ta sanar da hakan ta bakin mai magana da yawun hukumar, Ezekila Manzo kamar yadda ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP.
Manzo ya ce ambaliyar ta shafi gonaki masu yawa da girman su ya kai hekta 107,6000.
Bayanan da hukumar ta NEMA ta wallafa dai sun nuna cewa yawancin mace-macen shu fi shafar arewacin ƙasar.
Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da darakta-Janar ta Hukumar ta NEMA, Zubaida Umar, ta ce hukumar ta fara shirin aikin kwashe jama'ar da ke fuskantar barazanar ambaliyar ruwan sama zuwa kan tuddai.
Zubaida Umar ta ce ambaliyar ta shafi mutum 526,703 a ƙananan hukumomi 133, inda lamarin ya shafi gidaje 79,138 da kuma hekta 106,178 na gonaki.
China da Amurka na ƙoƙarin kyautata alaƙarsu
Asalin hoton, Getty Images
Shugaba Xi Jingping na China ya gana da mai bai wa shugaban Amurka shawara kan harkar tsaro Jake Sullivan a wani mataki da ke nuni da yiwuwar Karin dankon zumunci tsakanin kasasen biyu gabannin zaben shugaban ƙasan Amurka na watan Nuwamba.
Kalamai daga ɓangarorin biyu na nuni da cewa akwai ƴr jituwa tsakaninsu duk da bambance-bambancen da ke tsakaninsu kan al’amuran kasuwanci da batun yancin Taiwan, da kuma yakin Ukraine.
Mista Sullivan dai ya kwasahe kwanaki uku a China inda ya gudanar da muhimman taruka da ɓangarori daban-daban na gwamnatin kasar a yukurin da Amurka take yi na kara bunƙasa harkokin Diflomasiyya da China.
Ya ce wannan da gaske ziyara ce ta aiki, cikin sa’o’I 14
"Mun tattauna kan al’amura da dama da suka haƊa da barazanar sauyin yanayi da kuma yaƘin da muke yi da fataucin miyagun Ƙwayoyi inda muke ƘoƘarinmu daƘile yadda miyagun Ƙwayoyi ke kwara cikin Amurka".
Hotunan gidaje da gine-ginen da suka lalace bayan harin Isra'ila a Tulkarm
Ga wasu sabbin hotuna daga birnin Tulkarm da ke gabar yammacin kogin Jordan inda sojojin Isra'ila suka kai hari da ke nuna yadda gidaje da gine-gine suka lalace sakamakon harin.
Sojojin Isra'ila ɗin sun ce sun kashe 'yan ta'adda biyar da suka boye a cikin wani masallaci a lokacin da suka kai hari.
Asalin hoton, Reuters
Asalin hoton, Reuters
Asalin hoton, Reuters
Ambaliyar ruwa a Gujarat ta Indiya ta kashe mutum 28, ta raba dubbai da muhallansu
Asalin hoton, Reuters
Akalla mutum 28 ne suka mutu, sama da 24,000 kuma suka rasa muhallansu a jihar Gujarat da ke yammacin ƙasar Indiya sakamakon ambaliyar ruwa da yayi ƙamari tun ranar Lahadi.
Koguna da tafkunan ruwa da dama sun cika sakamakon ruwan sama kamar da bakin ƙwarya, dalilin afkuwar ambaliyar, in ji jami'ai.
Yayin da ake sa ran za a samu ƙarin ruwan sama a cikin kwanaki masu zuwa, jihar na cikin shirin ko ta kwana.
Gujarat akai-akai tana fuskantar mummunar ambaliyar damina wanda a cikin shekarar 2017, mutum 200 ne suka mutu sakamakon ambaliyar ruwa.
A cewar wani rahoto na gwamnati, sassa da dama na Gujarat na cikin haɗarin fuskantar ambaliyar ruwa saboda yawan manyan koguna da ke wurin.
Asalin hoton, Reuters
Asalin hoton, Reuters
Asalin hoton, Reuters
Sojojin Isra'ila sun kashe Abu Shujaa na ƙungiyar mayaƙan Falasɗinawa
Ɗaya daga cikin mayaƙan Falasɗinawa da aka kashe a Tulkarm, Muhammed Jabber, na ɗaya daga cikin manyan mayaƙan a yankunan Yamma da Kogin Jordan da Isra'ila ke zargi da ayyukan "ta'addanci".
Abu Shujaa kamar yadda aka fi sanin sa, an haife shi a sansanin ƴan gudun hijra na Nur Shams kuma shi ne kwamandan mayaƙan da ke Tulkram wani tsagi na ƙungiyar mayaƙanFalaɗinawa ta Palastenian Islamic Jihad.
Jabber ya yi hira da kafafen watsa labarai da dama a ƴan watannin nan, inda yake tattaunawa kan shekaru fiye da huɗu da ya kwashe a gidan yari da kuma yunƙurin kashe shi da dakarun Isra'ila suka yi a baya.
A watan Afrilu ne sojojin Isra'ila suka ayyana neman sa, inda kuma bayan kwanaki biyu sai aka gan shi a wata jana'izar wani ɗan gwagwarmaya.
Kawo yanzu babu tababa dangane da mutuwar tasa.
Dakarun Isra'ila sun ce an kashe Jabber ne tare da wasu mutum huɗu a cikin wani masallaci da suka ɓuya.
Dakarun sun zargi Jabber da kitsa harbe wani marar hula mai suna Amnon Muchtar a watan Yuni.
Ƙungiyar mayaƙan Falasɗnawa ta Palastenian Islamic Jihad ta ce Jabber ya yi shahada, inda kuma ta yi alƙawarin ɗaukar fansar kisan nasa.