City ta caskara United a wasan hamayyar Manchester

Foden

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Phil Foden ne ya zura ƙwallo biyu a ragar Manchester United a filin wasa na Etihad, inda Manchester City ta doke Manchester United da ci 3-1.

United dai ta fara wasan da kafar dama bayan da Marcus Rashford ya jefa ƙwallo a ragar City a minti na takwas da take wasa.

Amma daga baya Foden ya farɓe ragamar wasan inda ya jefa ƙwallo biyu bayan an dawo hutun rabin lokaci.

An ɗan yi ce-ce-ku-ce kan ƙwallon farko da Foden ya ci inda aka bai wa kocin United Erik Ten Hag katin gargadi saboda ya ƙalubalanci alƙalin wasa sakamakon karo da Rashford ya yi da Kyle Walker, yana mai cewa an yi wa ɗan wasansa ƙeta.

Wannan dai ita ce nasara ta shida da City ta samu kan United wasanni bakwai da suka buga a baya bayan nan, kuma wannan shi ne karo na 11 da United ta yi rashin nasara a kakar wasan bana.

Abu mafi mahimmanci shi ne sakamakon yana nufin ƙungiyar Pep Guardiola ta yanke tazarar da Liverpool ta ba ta a saman teburi zuwa maki ɗaya, kuma ƙungiyoyin biyu za su kece raini a filin wasan Anfield a ranar Lahadi mai zuwa.

United ta ci gaba da kasancewa a matsayi na shida a kan teburi, da tazarar maki 11 tsakaninta da Aston Villa da ke matsayi na huɗu kuma za ta karɓi baƙuncin Everton a wasanta na gaba.