Man United na kan turbar daukar Frankie de Jong

Asalin hoton, Getty Images
Manchester United ta cimma yarjejeniyar daukar dan kwallon Barcelona Frankie de Young kan fam miliyan 56 har da karin tsarabe-tsarabe.
Sai dai kungiyar ta sanar cewar ba a kai ga karkare komai ba, domin da akwai wasu batutuwa da ba a kammala su ba.
Sai dai kuma ana ganin cewar an hau kan turbar da za a iya karkare cinikin nan gaba kadan.
Dan wasan mai shekara 25, shi ne na farko da sabon kociyan Manchester United, Erik ten Hag ke son dauka a bana.
Ten Hag ya fara jan ragamar atisayen Manchester United a karon farko ranar Litinin, sai dai wasu manyan 'yan wasan ba su koma ba.
Haka kuma United tana jiran bayani daga dan wasan tawagar Denmark, Christian Eriksen, mai shekara 30, wanda Brentford ke fatan tsawaita kwantiraginsa.
Ten Hag da 'yan wasan United za su je Thailand da Australia ranar 8 ga watan Yuli, domin yin atisayen tunkarar kakar da za a fara a cikin watan Agusta.
United na fatan kammala cinikin De Jong kafin fara kakar bana, amma kawo yanzu ba a kai ga cimma matsaya ba.










