Matan Indiya da ke faɗa da kafa matatar man Saudiyya

Indian women
An wallafa

Dubban matan wasu ƙauyuka ne a jihar Maharashtra da ke yammacin Indiya, suka fantsama kan tituna cikin zafin rana don hana aikin gwaje-gwaje da wasu jami'ai ke yi a yunƙurin gina wata katafariyar matatar man fetur a yankin.

Mata masu yawa ne suka zaɓi aske gashin kansu, wasu kuma suka yi yajin cin abinci, a wani mataki na nuna adawa da ƙudurin kafa matatar.

'Yan sanda sun sanya dokar hana zirga-zirga tare da amfani da kulake da hayaƙi mai sa hawaye wajen tarwatsa masu zanga-zangar.

Haka zalika sun kama tare da tsare wasu mata 'yan gwagwarmayar nuna adawa da gina matatar.

''Ba ma son wannan matata da ke ƙunshe da sinadarai masu gurɓata muhalli. Ba za mu bari gurɓataccen mai daga wata ƙasar Larabawa ya ɓata mana gari ba'', in ji Manasi Bole.

Tana ɗaya daga cikin dubban masu zanga-zangar nuna adawa da shirin kafa wata matatar ɗanyen man fetur mafi girma a duniya cikin Indiya.

Matatar wadda ƙasar Indiya tare da haɗin gwiwar kamfanin man fetur na Saudiyya za su gina, za a kafa ta ne a wasu ƙauyukan yammacin Indiya.

Ƙauyukan masu albarkar bishiyoyin kayan marmari, da arziƙin kamun kifi, sun kasance wurare duwatsu da ke ɗauke da sassaƙe-sassaƙen tarihi.

A ƙarshen watan Afrilu ne aka ɓarke da zazzafar zanga-zanga a gundumar Ratnagiri ta jihar Maharashtra a yammacin ƙasar, lokacin da hukumomi suka fara gwaje-gwajen ƙasa domin gudanar da wannan gagarumin aiki.

Babban kamfanin man fetur na Indiya da haɗin gwiwar kamfanin mai na ƙasar Saudiyya wato Aramco da kuma kamfanin samar da man fetur na Haɗaɗɗiyar Daular Larabarawa ADNOC ne za su yi aikin gina katafariyar matatar man.

Nuna adawa da matakin

A faɗin ƙauyukan da wakilan BBC suka kewaya, sun ga alamun nuna bijirewa da kafa matatar man fetur ɗin a fuskokin mutane.

Sun faɗa mana cewa ƙasar wajen ba ta da kyau, kuma a nan suke samun ruwan sha musamman a lokacin bazara, wurare ne da suke shuka kayan marmari, don samun ‘ya’yan itatuwa’’, in ji Misis Bole.

y

Lokacin da yake zaune a cikin kwale-kwalen kamun kifinsa, Imtiaz Bhatkar ya ce ya damu game da yunƙurin kafa matatar, wadda ke barazana ga sana’ar da rayuwarsa ta ta’allaƙa a kai.

"Ba za a bar mu, mu yi su ba, ko da daga nisan kilomita 10 ne, saboda tankokin da ke ɗauke da danyen man fetur za su gurɓata ruwan’’, in Mista Bhatkar.

Ya ƙara da cewa "kusan mutum 30,000 zuwa 40,000 ne daga ƙauyukanmu da wasu wuraren suka dogara da sana’ar su. Idan hakan ta tabbata me mutanen nan za su yi?

Manoman mangoro a yankin - waɗanda suka shahara da shukar wani nau'in mangoro mai daraja da ake kira Alphonso - sun faɗa mana cewa ko yaya iska ta gurɓace, sannan aka sare dazuka, hakan na iya ɓata bishiyoyinsu sosai, bisa la'akari da saurin tasirin da mangoron Alphonso ke da shi ga kaɗawar iska da canjin yanayi.

Tasirin Siyasa

Duka gwamnatocin jihar Maharashtra da suka shuɗe na nuna goyon bayansu ga matakin, musamman a lokutan da suke kan mulki. Sai dai da zarar sun sauka sai su fara adawa da shi.

An fara ayyana gina matatar a 2015 cikin ƙauyen Nanar, kilomitoci kaɗan daga wurin da a yanzu ake ƙoƙarin kafawa a ƙauyen Barsu duk dai cikin gundumar Ratnagiri.

An sauya bigiren farko ne, saboda zafin adawa daga mazauna ƙauyen Nanar, da shugabanni da kuma ƙungiyoyin kare muhalli suka nuna

A bara ne kuma babban ministan jihar, Uddhav Thackeray ya sake bijiro da batun, inda ya bayyana ƙauyen Barsu a matsayin sabon wurin da za a yi aikin.

To amma yanzu da ba ya kan mulki sai ya canza matsayi, inda yake nuna goyon baya ga mazauna ƙauyen wajen nuna adawa da aikin.

b

Gwamnatin jihar ta yanzu wadda ta ƙunshi wani ɓangare na jam'iyyar Mista Thackeray da jam'iyyar BJP mai mulkin ƙasar, ta ce adawa da matakin gina matatar man, tsantsar siyasa ce kawai.

Ƙaramin ministan jihar Uday Samant ya ce "Wannan ba matata ce da ke gurɓata muhallai ba. Ministan masana'atu ya faɗa mana, don haka haƙƙina ne na wayar da kan mutane game da maganganun da wasu ke shaida musu a kan matatar''.

Ya ƙara da cewa saɓanin maganganun da ake yaɗawa, babu wata illa ga muhalli da matatar man za ta yi ga yankin, wanda ke cikin jerin wuraren da Hukumar Raya Al'adu ta Majalisar Dinkin Duniya ta ayyana a matsayin muhimmin abin tarihi.

Mista Samant ya ce tuni gwamnati ta samu eka 3,000 daga cikin eka 5,000 da ake buƙata domin gudanar da wannan gagarumin aiki.