Ba a ga taɓarɓarewar al'amura irin yanzu a zamaninmu ba - Maryam Abacha

Ba a ga taɓarɓarewar al'amura irin yanzu a zamaninmu ba - Maryam Abacha
An wallafa

A zantawa ta musamman da BBC albarkacin cikar tsohon shugaban mulkin sojan Najeriya, Janar Sani Abacha shekara 25 da rasuwa, uwargidansa ta nuna cewa maigidan nata jajirtaccen shugaba ne da ya kawo kwanciyar hankali da daidaituwar al'amura.

Abacha wanda ya rasu ranar 8 ga watan Yunin 1998, ya yi mulki ne daga 1993 har zuwa mutuwarsa lokacin da yake ƙoƙarin mayar da Najeriya kan tsarin dimokraɗiyya.

Abacha Family