FA Cup: Martial ba zai buga wa United wasan karshe ba

Asalin hoton, Getty Images
Dan kwallon Manchester United, Anthony Martial ba zai buga wasan karshe a FA Cup ba da kungiyarsa za ta kara da Manchester City saboda jinya.
Dan wasan tawagar Faransa ya ji rauni a wasan karshe na Premier League da United ta ci Fulham 2-1 a Old Trafford ranar Lahadi.
Idan United ta ci City a karawar karshe ranar Asabar, zai ba ta damar daukar kofi biyu a bana, bayan da ta lashe League Cup a cikin watan Fabrairu.
Haka kuma idan United ta lashe kofin bana zai hana City fatan daukar kofi uku a kakar nan, bayan da ta dauki Premier tana kuma harin Champions League.
United ce keda tarihin lashe kofi uku a Ingila karkashin Sir Alex Ferguson a 1999, wanda ya ci FA Cup da Premier League da kuma Champions League.
Martial ya ci kwallo shida ya bayar da biyu aka zura a raga a karawa 21 a Premier League a kakar nan.
Haka kuma wani dan wasan da ke jinya a United shine Antony, wanda ya ji rauni a fafatawar da United ta ci Chelsea 4-1.
Sai dai Erik ten Hag ya sanar ranar Lahadi cewar watakila mai shekara 23 dan kasar Brazil zai warke kafin wasan na karshe ranar Asabar.











