Diaby ya kusan kammala komawa Al-Ittihad ta Saudi Arabia

Asalin hoton, Getty Images
Ɗan wasan Aston Villa, Moussa Diaby na shirin kammala komawa Al-Ittihad kan kuɗi kusan fam miliyan 50.4m.
Dan wasan mai shekaru 25 ya je Saudi Arabiya, domin a gwada lafiyarsa da kuma kammala cinikin, bayan kakar daya da ya buga a Villa Park.
Diaby ya koma Villa ne daga Bayer Leverkusen kan mafi tsada a tarihin ƙungiyar, kan fan miliyan 51.9m a bazarar da ta gabata, amma koci, Unai Emery ya yanke shawarar sayar da ɗan wasan na Faransa.
Hakan na zuwa ne bayan da kulob din ya sake sayen Jaden Philogene daga Hull, inda ta biya fam miliyan 13.5 ga ɗan wasan Ingila a wannan watan kuma tana jin zai iya yin tasiri sosai kan dawowar sa.
Ziyarci shafin mu na Aston Villa
Diaby ya buga wasa 54 a Villa, inda ya zura kwallaye 10, kuma ya taimaka mata ta kare a matsayi na hudu a teburin Premier domin a bada da ta samun tikitin shiga gasar zakarun Turai ta Champions League ta bana.
Villa na sake fasalin 'yan wasanta kafin fara sabuwar kakar wasa ta bana, kuma ta sayar da dan wasan tsakiya, Douglas Luiz ga Juventus kan fan miliyan 42.4 a watan jiya.
Ta kuma ɗauki Samuel Iling-Junior da Enzo Barrenechea, yayin da mai ttsaron baya, Ian Maatsen ya koma Villa daga Chelsea kan fan miliyan 35 da ɗan wasa, Lewis Dobbin daga Everton a kan fan miliyan tara.
A ranar Talata kuma Villa ta kammala sayan ɗan wasan Everton, Amadou Onana kan fan miliyan 50.









