IPMAN ba ta yi mana adalci ba – NMDPRA

Asalin hoton, FAROUKAHMED/FACEBOOK
Hukumar kula da harkokin sarrafawa da tacewa da sufurin man fetur a Najeriya, NMDPRA, ta ce iƙirarin da ƙungiyar dillalan man fetur, IPMAN, ta yi cewa ba a biyansu kuɗaɗen dakon mai ba gaskiya ba ne.
Dillalan man fetur ɗin dai sun fara yajin aikin gargaɗi na kwana uku ranar Litinin, saboda zargin ƙin biyansu kuɗaɗen.
Sai dai a tattaunawarsa da BBC shugaban hukumar ta NMDPRA, Injiniya Farouk Ahmed, ya ce daga watan Disambar bara zuwa watan jiya sun biya mambobin ƙungiyar kuɗin dakon mai fiye da naira biliyan 100.
Injiniya Farouk ya ce babu watan da suke fashin biyan dilalan man kudadensu, don haka idan aka ce ba sa biya to wa ake bai wa kuɗaɗen?
'Babu wanda ake fifitawa kan wani'
Shugaban hukumar ya ce sun sha zama da shugabanni da mambobin IPMAN kan wannan batu na biyansu kuɗaɗensu na mai, kuma suna cika alkawura.
Ya ce bayan korafin cewa ana zaɓen masu ido-da-tozali wajen biyan kuɗaɗen, ya sa suka ɗauki matakin soma biyan kananan masu dillalai, ko a watan Agusta a cewarsa sun biya naira biliyan 20.
Farouk ya ce batun an yi wata takwas ba a biya wani ba, ba gaskiya ba ne, domin tsari suke bi kan jadawali na musamman da suke amfani da shi wajen bai wa mutane kuɗaɗensu.
Ya ce “idan za a faɗi gaskiya a faɗi, idan an yi kuskure a faɗi kuskure”.
Injiniya Farouk ya kuma kara da cewa, idan ma an samu jinkiri to laifi ba daga garesu ba ne.
Saboda suma akwai inda sai sun karɓo kuɗaɗen sannan za su biya, don haka duk kuɗin da ya shiga hannusu suna fitarwa.
End of Wasu labaran masu alaƙa da za a iya karantawa
Sharhi

Dambarwar rashin biyan kuɗaɗen dillalan man fetur abu ne da aka shafe watanni ana jayayya a kai.
Ko a lokacin tattaunawarsa da BBC shugaban ƙungiyar IPMAN reshan arewa maso yammacin Najeriya, Bashir Ahmed Dan-Mallam ya ce akwai ‘yan kasuwa da dama da suka karye saboda riƙe musu kuɗaɗensu da aka yi.
Wannan yanayi na da nasaba da wahalhalun mai da aka sha a baya, kafin sauki ya samu kwana nan a galibin yakunan Najeriya.
Duk da cewa hukumar NMDPRA na cewa tana biyan waɗannan kuɗaɗe, a yanzu yajin aikin gargaɗin da masu dakon mai suka shiga na sake ɗiga ayar tambaya kan a ina matsalar take.
‘Yan Najeriya dai sun tsinci kai cikin yanayi na wahalar mai mafi muni a tsawon lokaci abin da ya kai ga ana sayen man fetur da tsadar gaske a wajen ‘yan bunburutu, kafin daga bisani sauki ya samu.
Sai dai idan aka ci gaba da tafiya a haka babu mamaki dogayen layuka a gidajen mai su sake dawo wa.











