Zan tattauna da masu tayar da ƙayar baya idan na zama shugaban ƙasa - Peter Obi

Asalin hoton, Channels TV
Ɗan takarar gwamna a Jam'iyyar Labour a Najeriya Peter Obi ya ce zai buƙaci ya tattauna da duk wani ɗan gwagwarmaya ko kuma masu tayar da ƙayar baya da gwamnatin Najeriya ta ɗaure idan ya samu mulkin ƙasar.
Mista Obi ya bayyana haka ne a wani zauren tattaunawa da tambayoyi da gidan talabijin na Channels a Najeriya ya shirya ga ɗan takarar da mataimakinsa.
Ko da wani ya tambayi Mista Obi ko cikin waɗanda zai tattauna da su har da ƴan Boko Haram da ke jawo matsaloli a arewacin Najeriya da kuma ƴan ƙungiyar IPOB da ke kudu maso gabashin ƙasar, sai ya ce " Zan tattauna da dukansu, ko ma wace irin bindiga ce suke ɗauke da ita".
Mista Obi ya ce ko da mutum yana ɗaure a gidan yari ne zai je ya fito da shi domin su zauna su tattauna.
Mista Obi ya ce ya yanke hukuncin yin haka ne domin ganin cewa an samu zaman lafiya a ƙasar.
"Zan tattauna da waɗanda suke so a tattauna da su. Sai an kalli me ke jawo suke gwagwarmaya; batu ne na rashin adalci ko lamari ne na talauci ko rashin aikin yi," in ji Mista Obi.
Mista Obi ya bayyana cewa idan gwamnati ta soma mayar da hankali kan batun zama da tattaunawa da ƴan ƙasar, babu wani ɗan gwagwarmaya a duniya da zai samu wani dalili na tayar da zaune tsaye sakamakon duk wata buƙata an biya ta.
Najeriya dai ta sha fama da zanga-zanga ta masu son ɓallewa daga ƙasar kamar ƙungiyar IPOB masu iƙirarin kafa ƙasar Biafra.
Yanzu haka jagoran ƙungiyar Nnamdi Kanu na ci gaba da zama a tsare a hannun jami'an tsaron Najeriya kan wasu zarge-zarge ciki har da na ta'addanci.
Wasu abubuwa da Mista Obi ya yi tsokaci a kai
Mista Peter Obi ya bayyana cewa idan aka zaɓe shi a matsayin shugaban ƙasa a zaɓe mai tafe zai tabbatar da ya cire tallafin man fetur kamar yadda gwamnatin Shugaba Buhari ta shirya cire shi.
"Ina tabbatar muku da cewa zan cire shi nan take. Tallafin mai - na taba faɗa cewa - wani aikin laifi ne da aka shirya kuma ba zan bari a ci gaba da shi ba."
Haka kuma Mista Obi ya bayyana cewa zai yi duk mai yiwuwa domin ganin ya cire Najeriya daga cikin duhu ta hanyar gyara wutar lantarki.
Mista Obi ɗin ya ce zai yi haka ne ta hanyar kwafar matakan da Afrika Ta Kudu da kuma Masar suka ɗauka na samun dawamammar wutar lantarki.
Ɗan takarar ta Jam'iyyar Labour ya kuma ce idan ya samu nasara zai dama da mata a gwamnatinsa sakamakon irin ƙoƙarin da ya ce matan suna da shi wurin harkar gudanarwa.











