Ingila za ta buga Nations League ba tare da Foden da Palmer da Watkins ba

Asalin hoton, Getty Images
Phil Foden da Cole Palmer da kuma Ollie Watkins ba za su buga wa tawagar Ingila wasa biyu da za ta kara a Nations League ba.
Kociyan riƙon ƙwarya, Lee Carsley ya gayyaci ɗan wasan Manchester City, Foden cikin tawagar, amma bai samu zuwa ba, sakamakon jinya.
Ɗan wasan Chelsea, Palmer da na Aston Villa, Watkins sun halarci sansanin Ingila a St George Park, daga baya suka koma ƙungiyoyinsu, domin ci gaba da jinya.
Ingila za ta kara da Jamhuriyar Ireland a Dublin ranar Asabar 7 ga watan Satumba, kwana uku tsakani ta fafata da Finland a Wembley.
Shi ne wasan Ingila na farko da za ta yi, tun bayan rashin nasara a karawar karshe a hannun Sifaniya a Euro 2024 a Jamus a watan Yuli.
Hakan ya sa Gareth Southgate ya ajiye aikin, inda aka naɗa kociyan matasan Ingila ƴan kasa da shekara 21 a matakin riƙon ƙwarya.
Carsley ya gayyaci ƴan wasa da yawa cikin tawagar da ya haɗa da Angel Gomes da Tino Livramento da Morgan Gibbs-White da kuma Noni Madueke.
Ƴan wasa da suka haɗa da Gomes na Lille da na Newcastle, Livramento da na Nottingham Forest, Gibbs-White da na Chelsea, Madueke sun taka leda karkashin Carsley a matasan Ingila ƴan kasa da shekara 21.
Haka kuma ya gayyaci Jack Grealish, wanda ba a kira Euro 2024 ba, shima ɗan wasan Manchester United, Harry Maguire yana cikin tawagar.











