Guardiola na fatan City za ta ja ragamar teburi a Champions League

Champions League

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Kociyan Manchester City Pep Guardiola ya fayyace mahimmacin karewa a matakin farko a cikin rukuni a Champions League.

Mai rike da kofin na bara za ta karbi bakuncin RB Leipzig ranar Talata a wasa na biyar-biyar a cikin rukuni bayan da ta lashe dukkan wasa hudun da ta yi.

City da Leipzig duk sun kai zagayen 'yan 16 da za su ci gaba da buga gasar ta Zakarun Turai, illa dai ana bukatar wadda za ta yi ta daya da ta biyu a rukunin.

Guardiola ya ce: ''Ya kamata mu ci wasa ko kuma mu tashi canjaras''.

''Mun yi abin da ya kamata, ina murna da muka kai zagayen gaba tare da Leipzig, zuwa wasannin da za a ci gaba daga Fabrairu.

''Yana da mahimmaci ka kammala a matakin farko a rukuni. Mun kwana da sanin cewar a zagaye na biyu za mu fara kai ziyara, sannan mu karbi bakunci hakan dama ce da za ta ba ka dama''.

City ta je ta doke Leipzig 3-1 a wasa na biyu a cikin rukuni - sakamakon da ya bai wa kungiyar da ke buga Premier League jan ragamar rukuninsu.

Saboda haka City na fatan kada a doke ta a wasan, amma ko canjaras ta yi za ta ci gaba da zama ta daya a rukunin.

City tana mataki na biyu a Premier League, kuma ba ta yi rashin nasara a Etihad ba tun Nuwambar 2022.

Ita kuwa Leipzig tana ta biyar a teburin Bundesliga da tazarar maki 11 tsakaninta da Bayer Leverkusen, wadda take ta daya.