Gabriel Jesus ya gama buga Gasar Kofin Duniya a Qatar

Asalin hoton, Getty Images
An yi wa dan kwallon Arsenal, Gabriel Jesus tiyata cikin nasara, hakan na nufin ya gama buga wa Brazil Gasar Kofin Duniya da ake yi a Qatar.
Mai shekara 25 tare da Alex Telles sun ji rauni a wasan karshe a rukuni da Kamaru ta ci 1-0 ranar Juma'a.
Wasan da aka fara da shi kenan a babbar Gasar tamaula ta Duniya a Qatar, bayan da ya canji dan wasa a karawa da Switzerland da kuma Serbia a rukuni.
Arsenal ta sanar da cewar dan kwallon ya fara jinya, sai dai ba a fayyace ranar da zai koma taka leda ba, illa dai ya gama buga wasannin da ake yi a Qatar.
Jesus ya ci wa Arsenal kwallo biyar a dukkan karawar da ya yi mata a bana, bayan da ya koma Emirates daga Manchester City.
Brazil za ta kara da Croatia a wasan Quarter finals ranar Juma'a 9 ga watan Disamba, bayan da ta ci Koriya ta Kudu 4-1 ranar Litinin a wasan zagaye na biyu.
Croatia ta kai daf da na kusa da na karshe, bayan da ta ci Japan 3-1 a bugun fenariti, sakamakon da suka 1-1 a minti na 120 ranar Litinin.







