Liverpool na gogayya da Man City kan Kimmich, Arsenal na son Simons

Asalin hoton, Getty Images
Liverpool ta shiga gogayya da Manchester City kan sayen ɗan wasan tsakiya na Jamus Joshua Kimmich, mai shekara 28 daga Bayern Munich. (Bild)
Arsenal na zawarcin matashin ɗan wasan tsakiya na PSG da Netherlands Xavi Simons, mai shekara 20 wanda ke zaman aro a RB Leipzig, ko da za ta rasa ɗan gaban Wolves Pedro Neto, mai shekara 23, na Portugal. (Football Transfers)
Ba a sa ran Manchester United za ta sayi wani ɗan wasa da zai maye gurbin Anthony Martial, wanda ake ganin zai yi jinyar mako goma ta ciwon matse-matsi da aka yi masa aiki. (Mail)
Ƙungiyar ta Old Trafford na shirin haɗa fam miliyan 100 ta hanyar sayar da ƴan wasanta a bazaran nan, inda za ta fara da Mason Greenwood, wanda ke zaman aro a Getafe. (i Sport)
Brentford ta amince ta sayi mai tsaron ragar ƙungiyar Elfsborg ta Sweden Hakon Valdimarsson ɗan Iceland mai shekara 22 a kan fam miliyan 2.6. (Athletic )
Ƙungiyar Genoa ta gasar Italiya ta Serie A na son ɗan bayan Everton, Ben Godfrey ɗan Ingila. (Fabrizio Romano)
Haka kuma a shirye Everton ɗin take ta sayar da ɗan wasanta na tsakiya Amadou Onana, a watan nan har ma ta yi masa farashi fam miliyan 60, kuma Newcastle tana sonshi. (Football Transfers)
Luton Town na sha'awar ɗan wasan tsakiya na Coventry City Ben Sheaf, ɗan Ingila. (Teamtalk)
Fulham ta janye daga tattaunawa da Krasnodar a kan sayen ɗan wasan gaba na Colombia Jhon Cordoba, saboda gudun saba takunkumin da aka sanya na hana mu'amulla da ƙungiyoyin Rasha. (Football Transfers)
Bayern Munich ta haƙura da maganar sayen ɗan bayan Newcastle da Ingila Kieran Trippier. (ESPN)
Mai tsaron ragar Newcastle United da Slovakia, Martin Dubravka, na shawara a kan ci gaba da zamansa a ƙungiyar a bazaran nan. (i Sport)
Kwantiragin ɗan wasan tsakiya na Coventry City Callum O'Hare, ɗan Ingila, zai ƙare a bazaran nan, saboda haka ma har Southampton, da Burnley da kuma Leicester City, na duba yuwuwar ɗaukansa. (Mail)











