Chelsea ta nemi Benzema, Man Utd za ta sayar da taurarin ƴan wasanta

Karim Benzema

Asalin hoton, EPA

An wallafa

Chelsea ta gabatar da buƙatarta ta sayen Karim Benzema daga ƙungiyar Al-Ittihad ta Saudiyya. (Guardian)

Al-Nassr na shirin gabatar da tayi mai girma na sayen Casemiro, da tsohon ɗan bayan tawagar Ingila ta 'yan ƙasa da shekara 21 Aaron Wan-Bissaka, yayin da Manchester United ke shirin sayar da 'yan wasanta masu karɓar albashi mai yawa. (Mail)

Tuni daman aka yi watsi da tayin da Al-Nassr ta yi na fam miliyan 20 a kan ɗan bayan Tottenham da Brazil Emerson Royal, wanda a maimakonsa ta karkata ga Wan-Bissaka. (Telegraph)

Victor Osimhen ya nuna alamun cewa zai bar Napoli a bazaran nan, inda Chelsea, da Manchester United da kuma Real Madrid duk aka ce suna son ɗan wasan na Najeriya wanda yarjejeniyarsa a Napoli ta tanadi sayar da shi a kan sama da fam miliyan 100. (90 Min)

Ɗan gaban Manchester United na Ingila da ya tafi aro, Mason Greenwood, yana dab da tafiya Barcelona a bazara bayan ya taka wa Getafe leda. (Sun)

Nottingham Forest na tattaunawa da Borussia Dortmund a kan bayar da aron ɗan wasan tsakiya na Amurka Giovanni Reyna, mai shekara 21. (Athletic )

An gargaɗi kociyan Crystal Palace Roy Hodgson, cewa zai rasa aikinsa muddin ba a ga sauyi ba a sakamakon da ƙungiyar ke samu, bayan ya gana da shugabanta Steve Parish. (Guardian)

Napoli ta cimma yarjejeniyar karɓar aron ɗan wasan tsakiya na Aston Villa, Leander Dendoncker ɗan Belgium, ba tare da sharaɗin sayensa ba na dole a kan fam miliyan 7.7. (Fabrizio Romano)

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Newcastle na neman yi wa Tottenham yankan-baya a kan sayen matashin dan wasan gaba na Club Bruges, Antonio Nusa, mai shekara 18. Ana kallon matashin na Norway a matsayin wanda zai iya maye gurbin Miguel Almiron na tawagar Paraguay, wanda zai iya tafiya Al-Shabab ta Saudiyya. (Football Insider)

Fulham ta kwallafa ranta a kan sayen ɗan bayan Chelsea na Ingila Trevoh Chalobah, mai shekara 24. (Teamtalk)

Lyon tana son karɓar Arnaut Danjuma, na Netherlands, kasancewar ƙungiyarsa Villareal ba ta jin daɗin rashin sa shi sosai a wasa a Everton wadda ta karɓi aronsa. (Mail)

Manchester United na sha'awar ɗan gaban Bayern Munich na Kamaru Eric Maxim Choupo-Moting, mai shekara 34, da kuma ɗan gaba na gefe na Sporting Lisbon Marcus Edwards na Ingila. (Football Transfers)

Haka kuma ƙungiyar ta Old Trafford ita ce kan gaba wajen zawarcin ɗan gaban Bologna Joshua Zirkzee, na Holland mai shekara 22, duk da sha'awarsa da Arsenal ke yi. (Sun)

Newcastle na shirin sayen matashin ɗan wasan tsakiya na Manchester City Harrison mai shekara 18. (Athletic)