Me ya sa yankin Gabas ta Tsakiya ke da muhimmanci ga duniya?

Asalin hoton, Getty Images
Yankin Gabas ta Tsakiya waje ne da ke fama da rikicin siyasa kusan kodayaushe, to amma kuma yanki ne da yake da muhimmancin gaske ga duniya.
Wannan ne ya sa idan wata matsalar tsaro ko wani abu ya tashi a yankin nan da nan sai ya ɗauki hankalin duniya.
Wannan yanki ne da ya haɗa nahiyar Turai da Afirka da Asia, wanda kuma ya ƙunshi ƙasashe 17, ciki har da Saudiyya da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa da Masar da Isra'ila da Syria da Iran da Trukiyya da Yemen.
Kasancewar yankin a inda yake ya sa yake shafar abubuwa da dama da suka danganci siyasa da tattalin arziƙin duniya.
Cibiyar manyan addinan duniya
Yankin na Gabas ta Tsakiya ne cibiyar manyan addinan duniya biyu - Musulunci da Kiristanci, wanda hakan ke nufin miliyoyin mutane a faɗin duniya da ke bin waɗannan addinai suna bin abin da ke faruwa a yankin sau-da-ƙafa.
Ana ɗaukar ƙasashe irin su Saudiyya da Isra'ila da Iran da muhimmancin gaske a tarihinci ga waɗannan addinai biyu.
Birane kamar su Ƙudus da Makkah da Madina suna ɗaukar hankalin duniya zuwa wannan yanki na Gabas ta Tsakiya.
Birnin Ƙudus na da wani muhimmanci na daban kasancewa waje ne da Musulmi da Kiristoci da kuma Yahudawa ke darajawa.
Nan da nan rikicin Falasɗinawa da Isra'ila a kan birnin yake ɗaukar hankalin duniya.
Masallacin Al-Aqsa da ke birnin na Ƙudus, wuri ne da ke zaman matattarar rikici, saboda Yahudawa na iƙirarin cewa wajen ibadarsu ne, yayin da su ma Musulmi ke iƙirarin haka.
Ziyara da ƴansiyasar Isra'ila ke kai wa Masallacin na janyo rikici tsakanin ƴansandan Isra'ila da Falasɗinawa - wanda wannan shi ne ɗaya daga cikin dalilan da Hamas ta ce ta kai wa Isra'ila hari a watan Oktoba na 2023.
Matattarar makamashin duniya
Yankin Gabas ta Tsakiya wuri ne da yake da muhimmanci sosai ga tattalin arziƙin duniya, musamman ma ɓangaren mai da iskar gas.
Saudiyya ita ce ta ɗaya a duniya wajen samar da mai a kasuwar duniya.
Haka su ma ƙasashe irin su Iran da Iraqi da Kuwait da Oman da Qatar sun dogara ne ga mai a tattalin arziƙinsu.
Tun bayan da wani kamfanin Amurka ya gano rijiyar mai mafi girma a duniya a gabashin Saudiyya a 1938, tarihin yankin ya sauya.
Daga wannan lokacin mai ya zama ƙashin-bayan tattalin arziƙin duniya.
Ƙwararru sun ce kashi 30 cikin ɗari na mai da kashi 20 cikin ɗari na iskar gas da ake amfani da su a duniya daga Gabasta Tsakiya ake samu.
Wannan ne ya sa yankin ya zama mai muhimmanci da ƙarfin gaske ga tattalin arziƙi da tsare-tsare na duniya.

Asalin hoton, Getty Images
Kasuwancin duniya da hanyoyin jiragen ruwa
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Yankin Gabas ta Tsakiya ya kasance wata hanya mai muhimmancin gaske ga kasuwancin duniya.
Muhimman yankunan sun haɗa da Tekun Maliya da Tekun Bahar-Rum da Tekun India da Tekun Abaiya da kuma Mashigin Tekun Fasha.
Fitattun hanyoyin ruwa a yankin na Gabas ta Tsakiya sun haɗa da Mashigar Suez, da Hormuz da Bab-el-Mandab da kuma ta Aqaba.
A duk lokacin da yaƙi ya tashi ko aka shiga wani yanayi na zaman ɗar-ɗar na siyasa, waɗannan hanyoyi sukan kasance cikin haɗari da hakan kan shafi harkokin kasuwanci na duniya.
Misali sau da dama Iran na barazanar rufe Mashigar Hormuz inda mashigar tekun Fasha ta haɗu da mashigar Tekun Oman - muddin rikicinta da Isra'ila ya ƙazanta
Haka hare-haren da 'yan Houthi ke kai wa jiragen ruwan Isra'ila bayan da aka fara yaƙin Gaza sun haifar da tarnaƙi ga sufurin jirgin ruwa a Tekun Maliya.
Haka shi ma Mashigin Suez mallakar Masar, hanya ce mai matuƙar muhimmanci, wadda ta haɗa Afirka da Asiya, kuma sama da jiragen ruwa 20,000 ke bi ta hanyar a duk shekara.
An rufe hanyar tsawon wani lokaci bayan yaƙin kwana shida na 1967 tsakanin Isra'ila da ƙasashen Larabawa, amma Masar ta sake buɗe ta a 1975.
Isra'ila da yawan zaman ɗar-ɗar
Ɗaya daga cikin dalilan da suka sa yankin gabas ta Tsakiya ke ɗaukar hankalin duniya shi ne kafa ƙasar Isra'ila bayan yaƙin duniya na biyu.
Yahudawan da suka tsira daga kisan kiyashi na Hitler sun yi ƙaura zuwa Falasɗinu, inda suka kafa Isra'ila.
Tun daga wannan lokaci Isra'ila ta kasance cikin rikici da yaƙi da maƙwabtanta - irin su Masar da Syria da Jordan da Lebanon.
An kori sama da Falasɗinawa rabin miliyan -500,000, daga gidajensu, inda daga nan suka fara gwagwarmaya da makamai ta neman kafa ƙasarsu mai 'yancin kanta.
Ƙungiyoyi irin su Hamas da Islamic Jihad da PLO sun yi yaƙi da dama da Isra'ila.
PLO ta cimma yarjejeniyar zaman lafiya da Isra'ila, kuma yanzu ita ke gudanar da ikon a Gaɓar Yamma, amma kuma Hamas har yanzu ita take tafiyar da mulkin Gaza, kuma ta yi yaƙi da dama da Isra'ila.
Kafuwar manyan dauloli
Bayan faɗuwar Daular Usmaniyya (Ottoman Empire) a 1922, Birtaniya kusan ita ta mamaye yankin gabas ta Tsakiya.
Amma bayan yaƙin duniya na biyu, sai kuma Amurka ta zama ita ce ta fi iko a yankin.
Amurkar ta kafa sansaninta na soji a gabashin Saudiyya a 1945 - wannan shi ne sansanin sojin Amurka na farko a yankin.
A yau Amurka tana da sansanonin soji kusan 19 a ƙasashe da dama irin su Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa da Masar da Jordan da Bahrain da sauransu.
Akwai sojojin Amurka 40,000 zuwa 50,000 a waɗannan sansanoni.
Wannan ya nuna muhimmancin da yankin yake da shi a siyasa da kuma tsaron duniya.
Bayan Amurka, Birtaniya ita ce babbar ƙasar yammacin duniya mafi ƙarfi a yankin Gabas ta Tsakiya, inda take da sojoji da dama a Cyprus.
Haka ita ma Rasha, wata babbar mai tasiri ce a yankin, musamman a Syria da Masar.
Gwamnatin Bashar al-Assad a Syria ta ci gaba da zama a kan mulki ne da taimakon Rasha har zuwa 2025, duk da yunƙurin yamma na ganin bayan gwamnati - to amma daga ƙarshe dai ta janye.
A ƙarshe dai wannan yanki na Gabas ta Tsakiya, yanki ne mai matuƙar muhimmanci da ke ɗaukar hankalin duniya kusa a kodayaushe saboda addinansa da albarkatun ƙasa da kasuwanci da siyasar duniya.
Idanun duniya har kullum yana kan yankin na Gabas ta Tsakiya.









