Yadda mutane suka yi tururuwar tallafa wa matar da ta zaɓi mutuwa saboda tsadar rayuwa

- Marubuci, Daga Mansur Abubakar
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Abuja
- An wallafa
Shamsiyya Abubakar ta fara fitar da rai da rayuwa - matsin tattalin arzikin Najeriya ya sa tana fafutuka a kullum domin ciyar da iyalinta su tara.
Shamsiyya mai shekara 32 ta zaɓi dafa shinkafar afafata da masu kamfanin sarrafa shinkafa ke watsarwa idan suka gama gyara shinkafa saboda taurin da take da shi.
Matar, wadda take jego, ta shaida wa BBC cewa ta shiga ƙangin tunani saboda irin ƙalubalen rayuwa da ta shiga.
"Wasu lokutan nakan ce: Maimakon ci gaba da irin wannan rayuwa, zai fi dacewa na mutu ba?" kamar yadda ta faɗa a bidiyon da ya karaɗe Najeriya.
Amma tun da aka wallafa bidiyon a ranar Talata, mutane suke ta tururuwar zuwa gidanta domin ba ta tallafin abinci da kuɗi.
Yunƙurin da mutane suka yi na ba-zata domin taimaka mata ya "sauya rayuwarta", kamar yadda ta ce, lokacin da BBC ta sake tuntuɓar ta a karo na biyu.
"Ban taba ganin maƙudan kuɗi irin haka ba a rayuwata...Na yi matuƙar godiya.
"Na samu kuɗi daga mutane da dama, wasu kuma sun kawo buhun tsaftatacciyar shinkafa da masara, don haka muna da isasshen abincin da za mu ci yanzu," in ji ta.
Mai gidanta, Haruna Abubakar ya kuma bayyana farin cikinsa ga yadda rayuwarsu ta sauya.
"A ranar da aka naɗi bidiyon na BBC, ba mu da abincin da za mu ci, da ƙyar na basu naira ɗari biyar su sayi shinkafa," in ji shi.
"A yanzu, ina cikin farin ciki yadda rayuwarmu ta sauya kuma muna da isasshen abincin da za mu ci."

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Sani Isah, ɗaya daga cikin waɗanda suka kai kayan tallafi ga iyalin, ya ce labarin Shamsiyya ya sa ya zubar da hawaye. Isah ya ƙara da cewa hakan ya sa ya ji ya zama dole ya taimaka da abin da yake da shi.
"Ina ganin labarinta abin kunya ne ga shugabanninmu, na zubar da hawaye bayan da na kalli bidiyonta. Ta ya mutum zai yi addu'ar mutuwa a maimakon ci gaba da rayuwa kawai saboda abinci?" kamar yadda ya tambaya.
"Ina addu'ar wasu da suke cikin irin yanayinta suma su sami taimakon da suke buƙata da zai sauya rayuwarsu."
Najeriya dai na fama da taɓarɓarewar tattalin arziki mafi muni a tarihi abin da ya janyo matsin rayuwa da fusata al'umma.
A ranar Talata ne, dubban mutane suka fantsama kan titunan faɗin ƙasar domin yin zanga-zanga kan yadda gwamnati take tafiyar da tattalin arzikin ƙasar.
Tsadar farashin abinci na ci gaba da zama dalilin da ke harzuƙa jama'ar ƙasar.
Farashin shinkafa, wadda aka fi ci a Najeriya, ya ninka fiye da sau biyu cikin shekarar da ta gabata. Ba Shamsiyya kaɗai bace ta koma cin shinkafar afafata ba da ke a dagargaje da tsakuwa da kuma tauri - sauƙin farashinta ya taimaka wa iyalai da dama da ke fama da rayuwa a arewa.
Wau mutane da dama sun shiga halin yunwa, wasu kuma suna ƙayyade abincin da suke da shi.
Shamsiyya ta ce a yanzu tana da ci gaba da rayuwa saboda kyautatawar da mutanen da ba ta sani suka yi mata.
Ta shaida wa BBC cewa tana son fara kasuwanci da abincin da ta samu domin ta ci gaba da kula da iyalinta.










