Bayern Munich ta kammala daukar Matthijs de Ligt daga Juventus

Matthijs de Ligt

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Bayern Munich ta kammala daukar mai tsaron baya, Matthijs de Ligt daga Juventus.

Dan kwallon tawagar Netherlands, ya amince da kunshin kwantiragin da zai kare ranar 30 ga watan Yunin 2027.

Dan wasan wanda an yi ta alakanta shi da cewar zai koma Manchester United ko Barcelona ko kuma Paris-St Germain da taka leda.

Bayan da isa Jamus a karamin jirgin sama ya fada cewar ''Ina cike da murna kasancewa ta a kungiyar nan.''

Ya fara taka leda a 2016 ya kuma lashe Eredivisie da Dutch Cup ya kuma buga wasan karshe a Europa League a 2017.

De Ligt ya ci kwallo takwas a wasa 77 a Ajax, kungiyar da ya koma taka leda yana da shekara tara, kuma ya zama matashin kyaftin din kungiyar a Maris din 2018.

Shi ne ya ci kwallon da Ajax ta doke Juventus ta kai wasan daf da karshe a Champions League, inda ta yi rashin nasara a hannun Tottenham.