Equatorial Guinea ta dakatar da Emilio Nsue

Afcon 2023

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Hukumar kwallon kafa ta Equatorial Guinea ta dakatar da Emilio Nsue nan take, bayan kammala gasar cin kofin nahiyar Afirka.

An samu ɗan wasan, mai shekara 34 dumu-dumu cikin hatsaniyar rashin ɗa'a a babbar gasar tamaula ta Afirka da Ivory Coast ta karɓi bakunci.

Nsue shi ne ya lashe takalmin zinare, bayan da ya ci kwallo biyar a Afcon a wasa huɗu, yayin da aka yi waje da Equatorial Guinea a zagayen ƴan 16.

Haka kuma ɗan wasan tawagar da ake kira 'National Thunder', Iban Salvador shi ma an dakatr da shi.

Equatorial Guine ta ce Salvador mai shekara 28 yana da hannu a hargitsin da ya faru ranar 29 ga watan Janairu, bayan Guinea ta yi nasara da cin 1-0.

Hukumar ta ce a cikin hayaniyar har sai da ƴansanda Ivory Coast suka shiga tsakani, hakan ya ja tawagar ta yi lattin komawa masaukinta.

Ranar Lahadi Nsue ya je birnin Abidjan inda ya karɓi kyautar takalmin zinare da ya lashe, bayan da Ivory Coast ta ɗauki Afcon na bana,bayan cin Najeriya 2-1.

Ɗan wasan ƙungiyar Intercity, wanda ya taka leda a Birmingham City da kuma Middlesbrough, shi ne kan gaba a yawan ci wa ƙasar ƙwallye mai 22 a raga.

Equatorial Guinea za ta buga wasan neman shiga gasar cin kofin duniya a cikin watan Yuni.