Wasan ninƙaya a gasar Olympics, da wankan kumfar sabulu cikin hotunan Afirka

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Wasu daga cikin fitattun hotunan Afirka da na 'yan nahiyar a wasu sassan duniya.

.

Asalin hoton, Krisztian Elek / Getty Images

Bayanan hoto, Fitaccen mai zanen nan dan Afirka ta Kudu Breeze Yoko, tsaye gaban sabon zanen da ya yi a garin Margate ranar Laraba. Wata tawagar masu zane-zane ce ta buƙaci ya haɗa kai da su domin yin zanen a garin nasu.
.

Asalin hoton, Jung Yeon-Je / AFP

Bayanan hoto, Dan wasan kwallon tebur ɗan ƙasar Senegal Ibrahima Diaw ne ke kallon ƙwallon lokacin fafatawa da tawagar Wong Chun Tinga na yankin Hong Kong a gasar wasan Olympics da ke gudana a birnin Pari na Faransa a ranar Litinin. An tashi wasan 4-3.
,,

Asalin hoton, Amanuel Sileshi / AFP

Bayanan hoto, A ranar Asabar, wasu maza suka yi wasan wallon tebur a babban birnin ƙasar Habasha wato Addis Ababa.
,,

Asalin hoton, Clodagh Kilcoyne / Reuters

Bayanan hoto, A ranar Litinin, mai wasan ninƙaya 'yar Afirka ta Kudu, wato Tatjana Smith ta ke ninƙaya cikin kwami a gasar Olympic inda ta ke fatan yin nasara a ninƙayar mita 100
.

Asalin hoton, Evgenia Novozhenina / Reuters

Bayanan hoto, Ta yi gagarumar nasarar cikin alhini.
..

Asalin hoton, Mustafa Yalcin / Getty Images

Bayanan hoto, Nasara dadi gare ta, anan ta gatsa lambar zinaren da hakoranta, a wani ɓangare na farin cikin kai labari a gasar ta Olympic.
..

Asalin hoton, Mohamed Abd El Ghany / Reuters

Bayanan hoto, Yara na wasa cikin ruwan kumfa saboda tsananin zafin da ake fama da shi.
..

Asalin hoton, Benson Ibeabuchi / AFP

Bayanan hoto, 'Yan Najeriya sun fantsama titunan wasu biranen ƙasar domin zanga-zanga kan tsadar rayuwa, anan masu zanga-zangar ne a tirunan birnin Lagas a ranar Alhamis.
,

Asalin hoton, Paul Botes / AFP

Bayanan hoto, A ranar Asabar, kade-kade da bushe-bushe sun cika Jami'ar Afirka ta Kudu da ke birnin Pretoria, yayin da mai ba da umarni ɗan AmurkaWilliam Eddins ke jagorantar masu bushe-bushen lokacin atisaye ga ƙungiyar matasa ta Africa United Youth Orchestra.
.

Asalin hoton, Issouf Sanogo / AFP

Bayanan hoto, A Ivory Coast wani mai faskare ne ke faskaren itace a kusa da gaɓar tekun Abobodoume a ranar Talata.
..

Asalin hoton, Mohamed Abd El Ghany / Reuters

Bayanan hoto, A dai wannan rana, wata budurwa ke ratsa inda ruwa ke kwarara, yayin da ake tsananin zafi a gaɓar tekun Hurghada da ke ƙasar Masar...