Ya kamata abokan hamayya su ji tsoron Man City - Haaland

Asalin hoton, Getty Images
Erling Haaland ya yi kakkausan gargaɗi ga abokan hamayyar Manchester City bayan ya ci ƙwallo biyar a wasan da ƙungiyar ta doke Luton da ci 6-2 a gasar FA Cup.
Ɗan wasan na Norway, mai shekara 23, ya kafa tarihi a matsayin ɗan wasan City na farko da ya ci ƙwallo biyar a wasa guda fiye da sau ɗaya yayin da ƙungiyar Pep Guardiola ta tsallaka zuwa zagayen daf da na kusa da na ƙarshe.
Kwanan nan Haaland ya dawo bayan watanni biyu yana jinya kuma, bayan da ya ɗauki lokaci wurin tabbatar da ya dawo cikin ƙoshin lafiya, ya ce a shirye yake ya jagoranci wani yaƙin neman lashe manyan gasanni uku a City.
Bayan nasarar da City ta samu a kakar wasan da ta wuce, yanzu tazarar maki ɗaya ne tsakaninta da Liverpool wadda take mataki na ɗaya a gasar ta Premier kuma tana kan gaba da ci 3-1 a wasan da ta buga da Copenhagen a zagaye na biyu na gasar cin kofin zakarun Turai.
"Muna nan zuwa, kuma a shirye mu ke." Haaland ya shaida wa ITV.
Tsohon ɗan wasan gaba na Borussia Dortmund ya nuna cewa yana kan ganiyarsa yayin da ya yi wasan kura da masu tsaron bayan Luton a filin wasan Kenilworth Road.
Hudu daga cikin ƙwallaye biyar da Haaland ya ci a Luton Kevin De Bruyne ne ya taimaka masa yayin da ƴan wasan biyu suka sake nuna dalilin da ya sa suke cikin abokan wasa mafi ban tsoro a fagen ƙwallon ƙafa ta duniya.
A ranar Lahadi mai zuwa City za ta buga wasanta na gaba inda za ta fafata da Manchester United a filin wasa na Etihad a gasar Premier.











