An dakatar da Eto'o daga zuwa kallon wasannin Kamaru wata shida

Asalin hoton, Getty Images
Fifa ta dakatar da shugaban hukumar ƙwallon kafar Kamaru, Samuel Eto'o daga zuwa kallon wasannin kasar zuwa wata shida.
An hukuntan tsohon ɗan wasan Barcelona da Chelsea ne, sakamakon da aka same shi da laifin karya dokar ɗa'a karo biyu ta Fifa.
An hukuntashi ne sakamakon abin da ya faru a gasar kofin duniya ta matasa ƴan kasa da shekara 20 ranar 11 ga watan Satumba, inda Brazil ta doke Kamaru 3-1 a zagaye na biyu.
Kamar yadda Fifa ta fitar da jawabi, an yi kalamai na ɓatanci da nuna halin rashin ɗa'a daga ƴan wasa da jami'ai a karawar da aka yi a Bogota a Colombia, inda Eto'o ya halarci karawar.
Kenan an hana mai shekara 43 halartar duk wani wasan Kamaru na maza da na mata tun daga masu karancin shekaru zuwa babbar ƙungiya har wata shida.
Fifa ta ce hukuncin ya fara aiki nan take, ta kuma ce ta sanar da Eto'o kan wannan matakin da ta ɗauka.
Tawagar Kamaru za ta kara da Kenya gida da waje a wasan neman shiga gasar kofin Afirka 2025 da za a yi a Morocco, inda za su kara a cikin watan Oktoba.
Ranar Litinin Eto'o ya ja ragamar taron hukumar ƙwallon kafar kasar kan tsara yadda za su fuskanci Harambe Stars ranar 11 ga watan Oktoba.
Hukumar ƙwallon kafar Kamaru ba ta ce komai ba kan wannan batun.










