Za a buga wasa na 13 tsakanin Bayern Munich da PSG

Asalin hoton, Getty Images
Bayern Munich za ta kara da Paris St Germain a wasa na biyu a Champions League ranar Laraba a Jamus.
Ranar 14 ga watan Fabrairu, Bayern ta ci PSG 1-0 a Faransa ta hannun Kingsley Coman a zangon 'yan 16 a gasar ta zakarun Turai ta bana.
Wannan shine karo na 13 da za su kece raini a tsakaninsu a gasar ta zakarun Turai, Bayern ta ci shida, PSG ma karawa shida ta yi nasara ba canjaras ko daya.
Bayern tana da Champions League shida jimilla, ita kuwa PSG har yanzu na nema.
Bayern za ta buga karawar ba tare da Benjamin Pavard, wanda aka yi wa jan kati a wasan farko a Faransa.
Bayan Lucas Hernandez da Manuel Neuer da suka dade suna jinya, Nagelsmann ya kasance mai 'yan kwallo da yawa masu koshin lafiya, bayan da Josip Stanisic ya murmure.
Kociyan PSG, Galtier ya ziyarci Munich ba tare da mai tsaron baya, Presnel Kimpembe da ke jinya, shi kuwa Neymar ya gama buga wasannin bana, bayan da likitoci suka yi masa aiki a kafarsa ta hagu.
Sai dai PSG za ta fara wasa da Kylian Mbppe a cikin fili, wanda ya fara daga benci a wasan farko a Faransa.
Wasa 12 baya da aka kara tsakanin kungiyoyin biyu:
2022/2023 Champions League
- Paris St-G. 0 - 1 B Munich
2020/2021 Champions League
- Paris St-G. 0 - 1 Bayern Munich
- Bayern Munich 2 - 3 Paris St-G.
2019/2020 Champions League
- Paris St-G. 0 - 1 Bayern Munich
2017/2018 Champions League
- Bayern Munich 3 - 1 Paris St-G.
- Paris St-G. 3 - 0 Bayern Munich
2000/2001 Champions League
- Bayern Munich 2 - 0 Paris St-G.
- Paris St-G. 1 - 0 Bayern Munich
1997/1998 Champions League
- Paris St-G. 3 - 1 Bayern Munich
- Bayern Munich 5 - 1 Paris St-G.
1994/1995 Champions League
- Bayern Munich 0 - 1 Paris St-G.
- Paris St-G. 2 - 0 Bayern Munich









