Roberto Mancini ya yi ritaya daga kocin Saudiyya

Asalin hoton, Getty Images
Tsohon kocin Manchester City Roberto Mancini ya cimma yarjejeniyar raba gari da Hukumar Kwallon Ƙafa ta Saudiyya kan ajiye aikin horas da tawagar Saudiyyan.
Mancini mai shekara 59, ya fuskanci yanayi mara dadi a lokacin da yake aikin horaswar, wanda ya fara a watan Agustan 2023 bayan ya bar koyar da tawagar Italiya.
A wasan Saudiyya na farko a Asian Cup a watan Janairu, ya ce ya ajiye 'yan wasa uku ne saboda ana zargin suna da wasan da suke son bugawa da wanda ba sa so.
Tsohon kyaftin din tawagar Salman Al-Fajar, Sultan Al-Gannam da mai tsaron raga Nawaf Al-Aqidi dukansu sun musanta wannan iƙirari.
Yayin gasar cin kofin nahiyar, Mancini ya fice daga filin wasa gabanin bugun fenaritin da suka yi da South Korea wadda ta cire Saudiyyan, "Ya bayar da haƙuri saboda barin fili kan a tashi, na yi tsammanin an tashi."
Mancini ya yi ta koken cewa 'yan wasan gaba na ƙasar baya buga kwallo yadda ya kamata a gasar Saudi Pro, wanda ya yi fice da ɗaukar manyan 'yan kwallo daga nahiyar Turai.
Saudiyya tana ta fuskantar koma baya a wasannin neman gurbin gasar kofin duniya ta 2026 ƙarƙshin Mancini, yayin da ta yi canjaras mai ban mamaki da Bahrain da Indonesia da suke ƙarshen jadawali.






