Pochettino na harin United, Chelsea na nazarin Maresca

Mauricio Pochettino

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Mauricio Pochettino na son ci gaba da zama a gasar Premier ta Ingila bayan ficewarsa daga Chelsea kuma da alama yana sha'awar aikin Manchester United idan har ta sallami Eric Ten Hag. (Standard)

Manchester United za ta kori Erik ten Hag ko da kuwa ƙungiyar ta yi nasara a wasanta da Manchester City a gasar cin kofin FA a ranar Asabar. (Guardian)

Chelsea za ta tattauna da kocin Leicester City Enzo Maresca yayin da ta ke neman wanda zai maye gurbin Pochettino. (Standard)

Maresca na da farashin kusan fam miliyan 7.5 a kwantiraginsa da Leicester City. (Talksport)

Har ila yau, Chelsea ba ta cire rai kan zawarcin Roberto de Zerbi ba, wanda ya bar Brighton a ƙarshen kakar wasa ta bana. (Telegraph)

Borussia Dortmund za ta tattauna game da mayar da yarjejeniyar aro na Jadon Sancho daga Manchester United zuwa na dindindin bayan wasan ƙarshe na gasar zakarun Turai, amma siyan ɗan wasan mai shekaru 24 zai yi wahala saboda da farashin da kulob ɗin na Old Trafford ya ƙaƙabawa ɗan wasan. (Sky Sports Germany)

Bayern Munich za ta miƙa wa kocin Burnley Vincent Kompany kwantiragi har zuwa shekarar 2027 domin ya zama sabon kocinta, inda kulob din na Jamus a ya kai matakin ƙarshe a tattaunawar ɗaukar tsohon ɗan wasan na Belgium. (Sky Sports Germany)

Gian Piero Gasperini na shirin yin watsi da damar zama kocin Napoli tare da sanya hannu kan sabon kwantiragi da Atalanta bayan ya lashe gasar cin kofin Europa League. (L'Eco di Bergamo )

Ƙungiyoyin Saudiyya a shirye suke su jira har zuwa bazara mai zuwa don ƙoƙarin sayen ɗan wasan gaban Liverpool ɗan ƙasar Masar Mohamed Salah, mai shekara 31, da kuma ɗan wasan tsakiyar Manchester City na Belgium Kevin de Bruyne, mai shekara 32, kan kyauta idan ba su samu ƴan wasan biyu a bana ba. (Telegraph)

AC Milan da Juventus na sha'awar ɗaukar ɗan wasan baya na Borussia Dortmund ɗan kasar Jamus Mats Hummels, mai shekara 35, a matsayin kyauta. (Bild )