Jam'iyyar NNPP ta dakatar da ƴan majalisar tarayya huɗu daga jihar Kano

Asalin hoton, facebook/multiple
Jama'iyyar NNPP mai mulkin jihar Kano ta sanar da dakatar da Sanata Kawu Sama'ila da wasu ƴan majalisar tarayya uku daga jihar ta Kano.
Ƴan Majalisar da jam'iyyar ta kora su ne:
- Suleiman Kawu Sumaila - Sanata mai wakiltar Kano ta kudu
- Aliyu Sani Madakin Gini - Ɗan Majalisa wakilai daga mazaɓar Dala
- Sani Abdullahi Rogo - Ɗan majalisa mai wakiltar Karaye da Rogo
- Kabiru Alhassan Rurum - Ɗan majalisar wakilai daga mazaɓar Rano, Kibiya da Bunkure
A bayanin da ya yi wa manema labaru a ranar Litinin a Kano, shugaban jam'iyyar, Hashim Sulaiman Dungurawa ya ce jam'iyyar ta ɗauki matakin ne bayan samun ƴan majalisar da laifin ayyukan zagon ƙasa ga jam'iyyar.
A cikin bayaninsa, Dungurawa ya ce ƴan majalisar waɗanda aka zaɓa a ƙarƙashin jam'iyyar NNPP suna gudanar da ayyuka da suka ci karo da manufofi da ƙudurorin jam'iyyar.
Wannan na zuwa ne yayin da har yanzu jam'iyyar ke ci gaba da fama da rikicin shugabanci.

Asalin hoton, facebook/Sanata Kawu Sumaila
A tattaunawarsa da BBC, shugaban NNPP na jihar Kano ya ce yanzu jam'iyyar ta kafa kwamiti wanda zai duba batun dakatarwar wanda zai gayyaci sanatan da sauran ƴan majlisar wakilai uku domin yin bayani kan zargin da ake yi musu.
Wane laifi ƴan majalisar suka aikata?
An fara ɗora ayar tambaya kan biyayyan ƴan majalisar ga jam'iyyar ne bayan bikin da aka gudanar na auren ƴan Sanata Kawu Sumaila.
Dungurawa ya ce Sanata Kawu Sumaila ya gayyaci manyan ƴan jam'iyyar APC mai mulkin ƙaar, kuma mai hamayya a jihar Kano zuwa wajen bikin, ba tare da ya gayyaci shugabannin jam'iyyar NNPP ba.
"Abdullahi Ganduje na wajen, Ibrahim Shekarau na cikin wurin, saboda haka irin wannan akwai takaici"
"Wane irin saƙo ko darasi suke koya wa ƴan baya ke nan?
"A matsayina na shugaban jam'iyyar NNPP bai gayyace ni ba, shi ne muka ga hakan bai dace," kamar yadda Dungurawa ya shaida wa BBC.
Dungurawa ya kuma yi zargin cewa sanatan da ƴan majalisar tarayyar ba su halarci taron da jam'iyyar ta NNPP ta gudanar a Abuja ba.
"Mun yi taro kwanan nan a Abuja ba su je ba kuma ba su turo wakilci ba."
Martanin waɗanda aka kora
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
A a tattaunawarsa da BBC, Sanata Kawu Sumaila ya ce "ita kanta wannan jam'iyyar da waɗanda suka yi sanarwar, kotu tana cajin su da cewa su ba halastattun shugabannin jam'iyya ba ne, don haka ba su da iko ko damar ɗaukar wannan mataki."
A game da batun gayyatar da shugaban jam'iyyar ta NNPP ya bayyana a lokacin sanar da dakatar da ƴan majalisar, Sumaila ya ce "gayyata ce kawai ta zumunci... shi ke nan yanzu jam'iyya sai ta hana ka gayyaci mutane zuwa harkarka?"
A martanin da suka fitar, ƴan majalisar, waɗanda suka haɗa da Sanata Suleiman Abdurrahman Kawu Sumaila, da Kabiru Alhassan Rurum, da Aliyu Sani Madakin Gini da kuma Abdullahi Rogo, sun ce dakatarwar ba wani abu ba ne face "yaudarar siyasa domin kawar da hankalin al'umma daga rashin kataɓus ɗin shugabancin jam'iyyar ɓarin Kwankwaso."
Sanarwar ta ƙara da cewa jagoran jam'iyyar, Rabi'u Kwankwaso na amfani da "rarrabuwar kawuna a matsayin makami" wajen ci gaba da mallake jam'iyyar.
"Shi ya sa suka ɓuge da bin wannan hanyar ta dakatarwa maras tushe.
"Baya ga cewa wannan mataki haramtacce ne, wani yunƙuri ne kuma daga ɓarin jam'iyyar wanda aka riga aka sallama daga jam'iyyar NNPP, kuma bai ya da hurumi ko kaɗan na ɗaukar irin wannan mataki."
Ƴan majalisar sun buƙaci al'umma su yi watsi da wannan kora, sannan suka ce suna nan cikin jam'iyyar inda za su yi duk mai yiwuwa "wajen ganin jam'iyyar ta amfani al'umma ba kawai son zuciyar Kwankwaso da muƙarrabansa ba."











