Amurka da Burtaniya sun magantu kan yaƙin Ukraine

Asalin hoton, Getty Images
Shugaba Trump da Firaministan Burtaniya Keir Starmer, sun gana a fadar gwamnati ta White House, inda makomar yaƙin Ukraine ta kasance abin da suka bai wa fifiko.
Mista Trump ya ce ana samun cigaba a kokarin kawo karshen yaƙin da Rasha - sai dai yaƙi yarda da shawarar mara-baya ga girke sojojin Amurka domin taimakawa tsaron Ukraine domin kaucewa yiwuwar samun akasi nan gaba.
Mista Starmer - wanda yayin tayin girke sojojin Burtaniya a Ukraine - na son Amurka ta taimaka musu da tsaron sararin samaniya da bayanan sirri da kayayyakin aiki.
Amma Mista Trump ya fito karara ya nuna cewa ba shi da wannan ra'ayi tare da jadadda cewa Shugaba Putin mutum ne da za a iya yarda da shi, ba zai ci amanar yarjejeniyar da za a cimma ba.
A lokacin da ya ke yiwa 'yan jarida tsokaci, Mista Trump ya jadadda cewa kowa ya gaji, lokaci ya yi na daina kashe-kashe
" Ana ta kashe mutane babu gaira babu dalili a Ukraine da Rasha, kuma alkaluman mamata ya wuce tunani. An lalata makarantu, asibitoci da birane da ƙayyatattun wuraren tarihi da coci-coci marasa adadi.
"Kafin shiga wannan batu da kokarin kawo karshen kisan da ake aikatawa, na tattauna sosai da shugaba Putin ta waya, mun yi maganganu sosai cikin nasara irinsa na farko a tarihi.
"Kuma shi ma shugaba Zelensky da tawagata sun yi magana haka zalika da sakatare janar na Nato a lokuta da dama, kuma muna aiki sosai wajen ganin mun kawo karshen yakin.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
"Ina ganin an samu cigaba sosai komai na tafiya daidaidai.
Sir Keir Starmer ya yabawa Mista Trump saboda kokarin da ya ke nunawa wajen kawo zaman lafiya da daidata Ukraine da Rasha.
"Ka samar da yanayin da ya bude kofar cimma yarjejeniya zaman lafiyar da tarihi ba zai manta ba -- yarjejeniyar da nake da yakinin za a yi murna a Ukraine da sauran sassa na duniya. Wannan shi ne riba.
"Amma dole mu tabbatar komai ya tafi daidai. Masu iya magana a Burtaniya bayan yaƙin duniya na biyu na cewa ba wai nasara wajen cimma zaman lafiya ba, amma abin da zamu iya yi yanzu wajen tabbatar da dorewar zaman lafiya, ba zaman lafiyar da zai karfafa ko taimakawa masu mamaya ba irinsu gwamnatocin Iran gwiwa.
"Mun yarda cewa dole ne tarihi ya kasance daga bangaren mai neman zaman lafiya ba mai mamaya ba.
Shugaban Amurka dai ya yabawa shugaba Zelensky na Ukraine, bayan a baya ya bayyana shi da mai mulkin kama karya.
A yanzu haka Mista Zelensky ya isa fadar White House ta Amurka, inda ake saran shugabannin biyu za su rattaba hannu kan yarjejeniyar albarkatun kasa.










